Tawagar Najeriya ta yi rashin nasara a hannun Guinea Bissau da ci 1-0 a wasan neman shiga Kofin Afirka da suka buga a Abuja, ranar Juma’a.
Wasa ne na uku-uku a rukunin farko don neman gurbin shiga babbar gasar kwallon kafa ta Afirka da za a yi a Ivory Coast a 2024.
- CBN ya saki takardun kudi, ya bai wa bankuna umarnin aiki a karshen mako
- Akwai gwamnonin da za mu kama da zarar wa’adinsu ya kare — EFCC
Guinea Bissau ta ci kwallon ta hannun Tanguy Zoukrou a minti na 29 da fara wasa a karawar da suka yi a filin wasa na Moshood Abiola a Abuja, Nageria.
Da wannan sakamakon Guinea Bissau ta koma ta daya a rukunin farko da maki bakwai, bayan da ta ci Super Eagles da cin Sao Tome da canjaras da Saliyo.
Super Eagles ta koma ta biyu da maki shida, bayan nasara a kan Saliyo da Sao Tome.
Ranar Laraba Saliyo da Sao Tome suka tashi wasa 2-2 a daya karawa ta uku a rukunin farko.
Ranar Litinin 27 ga watan Maris Super Eagles za ta ziyarci Guinea Bissau, domin buga wasa na hur-hudu a rukunin farko.
Ita kuwa Sao Tome za ta karbi bakuncin Saliyo ranar Lahadi 26 ga watan Maris.