Babu shakka zamani ya zo wa nahiyarmu da sauyi, inda wasu daga cikin al’ummarmu na zamanin nan ba su san kima da darajar sarakuna ba, domin kuwa ba su san irin tsarin da ya gudana ba ta fuskarsu, kafin zuwan mulkin Turawa.
A cikin wannan rahoto an zo da dunkulallun bayanai game da matsayin sarakunan Kasar Hausa da tsarin sarautarsu da ayyukansu ga jama’a da kuma wasu hanyoyi da suke taimaka wa hadin kan al’ummarsu.
- ’Yan bindiga sun sace mahaifiyar dan takarar Sanatan APC a Kano
- Tsohon Hadimin Ganduje ya zama dan takarar Gwamnan Kano a PRP
Sarakunan Kasar Hausa suna da babban matsayi wajen tabbatar da hadin kai a tsakanin al’ummar wannan kasa.
Har ila yau, suna daga cikin rukunonin jama’a wadanda suke ba da himma da kwazo wajen tattara hankalin mutane a waje daya, su zama suna ci daga akushi daya da kuma kwarya daya.
Ashe ke nan yana da kyau a gabatar da nazarin a rubuce game da hanyoyin da sarakuna suke amfani da su ta fuskar hada kan mutanen kasashensu, domin haka wannan takarda an ba ta suna, “Gudunmawar Sarakuna Wajen Hada Kan Al’umma.”
Kasar Hausa, kasa ce mai fadin gaske, wadda take kunshe da al’ummomi mazauna wurare daban-daban a cikin manya da kananan garuruwa.
Bisa dukkan alamu, Hausawa su ne mazauna farko, inda daga bisani suka gauraya da wasu al’ummomi, bayan da suka shaku da juna suka zama daya.
Harshe da manyan al’adu sun kara sanya Hausawa su zama al’umma daya, duk da bambance-bambancen akidun gargajiya da ake da su a da can.
Bayan zuwan addinin Musulunci, akasarin Kasar Hausa ta kasance mai bin tafarkin addinin Musulunci.
Jihadin Shehu Usmanu Dan Fodiyo (Allah Ya yi masa rahama) da tsayuwar Daular Musulunci wadda a yanzu ake kira Daular Usmaniyya, sun kara sanya Kasar Hausa ta zama dinkakkiyar kasa, mai magana da harshe daya.
Kamar yadda tarihi ya nuna, a da can a Kasar Hausa, kowane birni ko gari yana da tsarin shugabancinsa, wanda yake aiwatarwa bisa cin gashin kansa kuma sarki shi ne kan gaba a kowane gari, shi ne majibincin al’amuran mutanen wannan gari.
Daga nan ne aka samu sarki da sarauta da tsare-tsarenta.
Sarauta: Kalmar sarauta tana da ma’anoni daban-daban. Amma dukkan wadannan ma’anoni za a ga sun ginu ne a kan wasu shika-shikai gudauku, wato shugabanci da mulki da kuma iko.
Shugabanci dai shi ne yi wa mutane jagora a harkokinsu na zaman tare.
Mulki kuma ya danganci yawan jama’ar da mutum ya shugabanta da yaduwarsu da kuma girman muhallin da suke zaune a ciki da karfin jagorancin da yake iya yi masu.
Sukunin bayar da umarni da hani da tsaro kuwa shi ne iko.
Don haka a takaice, sarauta ita ce shugabantar jama’a don kiyaye addininsu da tafiyar da harkokin siyasarsu da samar masu hanyoyin jin dadin rayuwa masu kyau da kyautata hanyoyin tattalin arzikinsu da duk wasu al’amura na yau da kullum, musamman da dan Adam zai bukata na inganta rayuwarsa.
Domin haka sarauta ta kunshi shugabanci da mulki da iko.
Tsarin Sarauta: Tsarin sarautar Kasar Hausa kusan a yanzu yana iya zama hawa hudu, wato mai unguwa zuwa dagaci zuwa hakimi zuwa sarki da ’yan majalisarsa.
Haka kuma kowanne yana da ayyukan da suka rataya a wuyansa.
Ayyukan mai unguwa sun hada da kai rahoton duk wani abu da ya faru a unguwa, mai kyau da akasin haka, irin su fari ko ta’adin farin dango da sauransu.
Haka kuma alhakinsa ne ya ga cewa wasu ayyuka na assha ba su auku ba. Kuma alhakinsa ne ya tattaro kudin haraji da na jangali ya kai wa dagaci.
Ayyukan dagaci kuwa sun hada da ganin an samu kwanciyar hankali. Sannan shi yake sanar da hakimi labarin wani abu na alheri ko akasi, kamar annoba da makamantansu.
Dagaci ba ya yin shari’a amma alhakinsa ne ya binciki abin da ya faru, idan rashin fahimta ne, ya yi kokarin sasantawa; idan kuma abin mai girma ne sai ya aika da su zuwa ga hakimi.
Haka kuma alhakinsa ne ya lura da duk wani bako da ya zo yankinsa, ta hanyar mai unguwa. Bayan haka, shi ne yake shirya ayyukan taimakon kai-dakai, domin ci gaban yankinsa.
Shi yake tattara kudaden shiga, musamman haraji da jangali ya aika wa hakimi.
Ayyukan hakimi kusan daya ne da na dagaci, sai dai shi ba ya yin hulda da jama’a kai-tsaye kamar dagaci.
Alhakinsa ne ya sanar da sarki labarin faruwar duk wani abu (muhimmi) a gundumarsa. Wato shi yake harhada dukkan bayanan da dagatansa suka aiko masa, sannan ya isar da su wurin sarki.
Kafin samuwar alkali, yana yin shari’a kuma bayan samuwarsa, a karkashinsa yake.
Kamar na kasa da shi, idan ya tattara dukkan kudaden shiga, yana aikawa da su zuwa ofishin sarki (baitul mali).
Dangane da ayyukan sarki kuwa, idan hakimai suka kammala komai, shi suke aika ma wa, musamman abubuwan da suka danganci kudaden shiga.
Daga lokacin jihadi kuma, shi ma sarki sai ya koma karkashin Sarkin Musulmi da ke Sakkwato, wato bayan kafuwar Daular Usmaniyya.
Babu shakka akwai cikakkiyar hikima dangane da ayyukan shugabannin Hausawa.
Misali, mawuyacin abu ne dagaci ya kula da dukkan mutanen da suke yankinsa saboda yawansu. Don haka kasancewar mai unguwa zai taimaka gaya wajen tafiyar da mulkin ta hanya mai sauki.
Haka kuma abin yake dangane da hakimi da kuma sarki.
Don haka a iya cewa daya daga cikin hikimomin wannan tsari shi ne taimakekeniya, ta yadda za a sami saukin tafiyar da mulki.
A wannan jirwaye mai kamar wanka, marubucinmu kuma saraki, MALAM IS’HAKA SARKIN FULANI DANKAMA (08100006858), ya yi kokarin warware zare da abawa.