✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gostomel: Rasha ta kashe Magajin Gari a kusa da Kyiv

Magajin Garin Gostomel ya rasu a wurin raba wa marasa lafiya da gajiyayyu burodi a safiyar Litinin.

Sojojin Rasha sun kashe Magajin Garin Gostomel da ke kusa da Kyiv, babban birnin kasar Ukraine.

Hukumomin Ukraine sun ce an kashe Magajin Garin na Gostomel, Yuri Illich Prylypko, ne a safiyar Litinin bayan ya fita rabon burodi ga marasa lafiya da mutanen da ke fama da yunwa a garin.

“Magajin Garin Gostomel, Yuri Illich Prylypko, ya rasu ne a yayin da yake rabon burodi ga mayunwata da marasa lafiya,” kamar yadda hukumomi suka sanar ta Facebook.

Sanarwar ta bayyana cewa Prylypko da wasu mutum biyu sun gamu da ajalinsu ne bayan sojojin Rasha sun bude musu wuta.

“Babu wanda ya matsa mishi ya tunkari makaman masu mamayar; Amma ya ba da ransa saboda al’ummarsa da kuma garin Gostomel. Hakika ya rasu a matsayin gwarzo,” inji sanarwar.

A garin Gostomel, da ke Arewacin Kyiv ne filin jiragen saman soji na Antonov yake. 

Idan ba a manta ba, a filin jirgin na Antonov ne aka gwabza kazamin yaki tsakanin sojojin Rasha da Ukraine a farkon yakin kasashen biyu.