✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gombe United ta lallasa Kano Pillars a Firimiyar Najeriya

Kano Pillars ta makale a mataki na 13 da maki 24 a gasar Firimiyar ta bana.

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta kwashi kashinta a hannu yayin wasan mako na 20 da suka fafata da Gombe United a gasar Firimiyar Najeriya.

Gombe United ta yi wa Pillars da ake yi wa lakabi da sai masu gida ci daya mai ban haushi.

Filin wasa na Pantami shi ne dai ya karbi bakuncin wasan da ya gudana a ranar Lahadi 03 ga Afrilun 2022.

Dan wasa Barnabas Daniel ne ya zura kwallon a minti na 65 a karawar da aka shafe minti 90 ana bugawa tsakanin kungiyoyin da suka fito daga Arewacin Najeriya.

Nasarar da Gombe United ta yi ya sa ta koma mataki na 9 a teburin gasar da maki 27 a wasanni 20 da suka fafata.

Ita kuma Kano Pillars ta kasance a mataki na 13 da maki 24 a wasanni 20 da ta buga a kakar wasannin ta bana.

Yanzu haka dai Rivers United ita ce a matakin farko a teburin gasar da maki 43 a wasa 20 da ta buga.