✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gombe da Kano sun yi nasara a musabakar Alkur’ani a Abuja

Sun samu kyautar dubban daloli da kujerun zuwa aikin Hajji.

An bayyana wasu zakakurarrun matasa biyu ’yan Jihar Kano da Gombe a matsayin wadanda suka yi nasarar lashe musabakar Alkur’ani mai tsarki wadda Gaskiya TV ta shirya kuma ta kasance ta farko wacce ba gwamnati ba ce ta dauki nauyi ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, musabakar wacce aka shafe kwana uku ana yinta ta gudana ne a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.

Alhaji Hamza Tanko, wani dan kasuwa dan asalin kasar Ghana, shi ne ya dauki nauyi tare da shirya gasar a karon farko a Najeriya.

Tanko wanda ya ce sha’awar Alkur’ani ce ta zaburar da shi ya shirya gasar karatun Alkur’ani da aka saba gudanarwa duk shekara a kasarsa ta Ghana da aka fara gudanarwa tun bara.

Ya ce yana fatan musabakar ta zama wacce za a rika gudanar wa  duk shekara a kasashen Yammacin Afirka guda shida da nufin zaburar da yaran Musulmi su rika shagaltuwa da karatun Alkur’ani.

A cewarsa, hakan zai kawar da yaran Musulmi daga aikata munanan dabi’u na zamantakewa da sauran abubuwan da ba su dace ba.

“Ina da kudurin ganin an yada karatun Alkur’ani tare da kwadaitar da matasa zuwa ga karatun littafin mai tsarki,” in ji shi.

Daga cikin wadanda suka nuna bajinta, akwai Mubarak Aliyu mai shekara 20 daga Jihar Gombe da ya zama zakara a musabakar karatun Izu 60 kuma ya samu kyautar dala 5,000 da kuma kujerar aikin hajji ta bana.

Ya ce, “Na yi matukar farin ciki da kasancewa wanda ya lashe wannan musabakar karatun Alkur’ani bangaren Izu 60. Ba zan iya ko bayyana farin cikina ba, gaskiya.

“Kuma ina kira ga wadanda muka shirya gasar tare da su kara himma su kuma dage da addu’a har sai sun kai ga gaci; za su iya ma yin fiye da abin da na cimma.”

Hakazalika, Aisha Abubakar Hassan mai shekara 16 daga Jihar Kano ta zama zakara a bangaren Izu 30 da mata suka fafata.

Aisha Hassan yayin karbar kyautar da ta lashe.

Ta kuma bayyana jin dadinta tare da gode wa Allah da Ya sa ta samu nasara a wannan fanni yayin da ta yi kira ga sauran da suka fafata a gasar da su kara himma da addu’o’i su ma.

Ita ma an ba ta kyautar dalar Amurka 5,000 da kujerar Makka.

Haka nan ma wadanda suka zo na biyu da na uku sun samu kyautar dala 4,000 da 3,000 tare da kujerun Makka; yayin da na hudu da na biyar suka samu kyautar dala 2,000 da 1,000.

Babban mai kula da musabakar karatun Alkur’ani na Yammacin Afirka Abdulshakur Abbas, ya ce mutum 10 da suka zama zakaru a gasar za su wakilci Najeriya a musabakar da aka shirya a matakin kasashen Yammacin Afirka shida da za ta gudana wata mai zuwa a kasar Ghana.

Dukkanin wadanda suka halarci musabakar sun kasance ‘yan kasa da shekaru 20, inda maza 20 da suka halarci karatun Alkur’ani cikakke na Izu 60, yayin da mata suka fafata a musabakar Izu 30.

Aminiya ta ruwaito dalibai 40 ne suka halarci musabakar da suka fito daga jihohin Arewa da kuma babban birnin tarayya Abuja in banda Jihohin Kogi da Benue wadanda ba su aiko wakilansu ba.

Manyan Sarakunan Arewa da dama daga sun halarci gasar ciki har da Sarkin Musulmi wanda Wazirin Sakkwato ya wakilta — sun halarci bikin.