✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Golan Najeriya na farko ya rasu

Golan Najeriya na farko mai suna Sam Henshaw Ibiam ya rasu. dan kimanin shekara 90 Henshaw Ibiam ya rasu ne a shekaranjiya Laraba a gidansa…

Golan Najeriya na farko mai suna Sam Henshaw Ibiam ya rasu. dan kimanin shekara 90 Henshaw Ibiam ya rasu ne a shekaranjiya Laraba a gidansa da ke kauyen Afikpo da ke Jihar Ebonyi.
Tsohon golan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya da ake kira da Red Debil a wancan lokaci ba a bayyana takamaiman dalilin mutuwar tasa ba.
Rahotanni sun nuna a tsawon lokacin da marigayin ya yi wa Najeriya kwallo, an zura masa kwallaye biyar ne kacal a raga kafin ya yi ritaya a shekarar 1958. Ana yi wa marigayin lakabi ne da “The Black Magnet” ko “The Cat” a lokacin da yake gola sakamakon bajintarsa da kuma kwarewarsa.
 An ce marigayin ya fada cikin tarkon talauci tun bayan da ya yi ritaya inda aka nuna yana zaune ne a wani  bangare na  gidansa da bam ya lalata a lokacin yakin basasa kuma har ya rasu bai samu sukunin gyara wannan bangaren ba.  Haka kuma babu wani ko wasu da suka taimaka masa wajen gyara gidan nasa.
Ashekarun baya ne dai tsohon golan ya samu nasarar lashe kyautar Naira miliyan 1 a wani shiri da Kamfanin sadarwa na MTN ya dauki nauyi a gidan talabijin na kasa (NTA) wanda ake wa lakabi da “Who Wants To Be A Millionaire”, watau “Wa Ke Son Ya Zama Miloniya”.
Tuni Dokta Sanusi Mohammed Sakatare-Janar na Hukumar NFF ya tabbatar da mutuwar golan, inda ya mika sakon ta’aziyya a madadinsa da kuma hukumar NFF ga iyalan mamacin.