✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Golan Brazil ya tsallake rijiya da baya

A ranar Asabar da ta wuce ne golan Brazil Jefferson ya kusa mutuwa bayan ya yi arba da wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton…

A ranar Asabar da ta wuce ne golan Brazil Jefferson ya kusa mutuwa bayan ya yi arba da wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan fashi da makami ne a kan hanyarsa ta zuwa yin atisaye a Brazil.

Kamar yadda rahotannin da ke fitowa daga Brazil suka nuna, an ce dan kwallon yana kan hanyarsa ta zuwa yin atisaye ne da sanyin safiyar Asabar sai ya ci karo da ’yan fashi da makamin inda suka tare shi sannan suka yi awon gaba da motarsa kirar SUb da kudin da ba a tantance adadinsu ba sai dai ya yi sa’a ba su taba lafiyarsa ba.

An ce jami’an tsaron sun samu bayanin fashin ne a kyamarorin da aka dasa a asirce (CCTb) inda aka ga yadda fashin ya gudana ga dan kwallon.

Jim kadan bayan al’amarin ya faru dan kwallon ya yi amfani da shafin sadarwarsa ta Instagram wajen sanar da al’amarin. Jefferson dan shekara 34 ya yi wa Brazil gola ne a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015 inda ya kama wa kasarsa kwallo har sau 22.

Sai dai wani rahoto ya ce  tuni jami’an tsaron suka yi nasarar gano motar a wani yanki da ake kira Fazedinha amma ba su yi nasarar kama kowa ba.

Sannan Jefferson ya taba yin kwallo a kasar Turkiyya a tsakanin shekarar 2005 zuwa 2009 inda ya buga wa kulob din Trabzonspor da na Konyaspor.

Ya zuwa hada wannan rahoto, jami’an tsaro sun cigaba da zurfafa bincike don zakulo wadanda suka aika fashin don a hukunta su.

Al’amarin ta’addanci a kasar Brazil ba sabon abu ba ne, don kasa ce da ke fama da na’ukan ta’addanci da suka hada da fashi da makami da safarar miyagun kwayoyi da fyad da sauransu.