Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta Jihar Kano (KAINSEC) ta ce tuni shirye-shirye sun kammala na gudanar da zaben shugabanin Kananan Hukumomi da kansiloli a jihar wanda za a yi a gobe Asabar.
Shugaban Hukumar Farfesa Ibrahim Garba Sheka ne ya bayyana haka a lokacin da ake gudanr da taron bita ga jami’an d za su gudanar da zaben na gobe.
Farfesa Ibrahim Sheka ya bayyana cewa hukumar ta kammala raba dukann abubuwan da ake bukata a wajen zaben “kayayyakin zabe tni suka isa dukanin wuraren da za a gudanr da zaben. Da za a ce a yanzu ma a gudanar da zaben to da za mu iya gudanar da shi ba tare da fargabar komai ba”
Ya yi kira ga jami’an da za su gudanar da zaben da su kasance masu kula da nauyin da aka dora musu tare da gudanar da shi bisa gaskiya da amana.
A wani ci gaban kuma Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta bayyana cewa ta girke jami’an ‘yan sanda dubu 12 wadanda za su samar da tsaro a lokacin zaben na gobe Asabar.