Bayan kammala zaben Gwamnan Jihar Kebbi na 18 ga Maris, inda jam’iyyyun APC da PDP suka fi yawan kuri’a, sai aka bayyana sakamakon zaben da bai kammalu ba.
Dokta Nasiru Idris Kauran Gwandu ne dan takarar APC, da ke karawa da Manjo Janar Aminu Bande (mai ritaya) na PDP.
- Karasa Zabe: Za mu samar da tsaro a Kano —’Yan sanda
- Karashen Zabe: INEC ta raba kayan aikin zabe a Adamawa
Baturen zabe a Jihar Kebbi, Farfesa Yusuf Sa’idu ya ce za a sake zabe a wasu rumfuna a kananan hukumomi 20 daga cikin 21 a sakamakon zaben da ya bayyana Jam’iyyar APC ce ke gaban PDP da tazarar kuri’a sama da dubu 45.
Kakakin Kwamitin Zaben APC a Jihar, Alhaji Kabiru Sani ya ce ba a yi musu adalci ba, inda ya bukaci a canja Baturen Zaben.
Ya ce sakamakon zaben da hukumar ta bayyana APC da Alhaji Idris sun samu kuri’a dubu 388,258, sai PDP ta samu dubu 342,980.
Ya ce don haka bai kamata a bayyana zaben cewa bai kammalu ba, “Domin dan takararmu ya ba da tazara kuri’a dubu 45 da 278, a wasu jihohi an sanar da wanda ya yi nasara da tazara da ba ta kai haka ba,” in ji shi.
Alhaji Umaru Gwandu na Jam’iyyar PDP ya ce suna da tabbacin za su ci zaben domin mafi yawan inda ba a yi zabe ba su ne ke da rinjaye.
Ya ce abin da suke so, a bari a yi zabe cikin lumana mutane su zabi wanda suke so za a ga wannan tazarar ba komai ba ce.
A Jihar Adamawa, Baturen Zaben, Farfesa Mohammed Mele ne ya sanar da zaben 18 ga Maris da wanda bai kammalu ba.
An fafata zaben ne tsakanin Gwamna Ahmadu Fintiri na PDP da Sanata A’ishatu Binani ta APC.
Jami’in zaben ya ce wanda ya yi nasara ba zai iya fitowa ba, saboda adadin kuri’un zabe na da aka karba a rumfunan 69 da zaben Gwamna bai gudana ba ya haura kuri’a 31,250 da Fintiri ke kan gaba da su.
Gwamna Fintiri ya samu kuri’a dubu 421 da 524, Sanata Binani ta samu kuri’a dubu 390 da 274 a kananan hukumomi 21 na Jihar Adamawa.
Wannan shi ne karo na biyu da Fintiri ke takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP.
Ko a shekarar 2019 haka aka yi, inda aka bayyana zaben Gwamnan da bai kammalu ba a takarar da aka yi tsakanin Gwamna Mohammed Jibrila Bindow a wancan lokaci da Ahmadu Fintiri.
Sai dai Gwamna Fintiri ne ya samu nasara a zabe na biyu. A 2019 Fintiri ya samu kuri’a dubu 376 da 552 shi kuma Bindow ya samu kuri’a dubu 336 da 386.
Karamar Hukumar Numan da ke Kudancin Jihar, ita ce ke da jiga-jigan Jam’iyyar PDP tun dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999, inda babu wata jam’iyya da ta lashe Numan.
Masu zabe 7,357 da suka cancanci kada kuri’a ne za su jefa kuri’a a sake zaben a Numan. Wannan ya sa ake tunanin Numan ce za ta iya zama raba-gardama, inda ake tunanin APC za ta yi kokarin kutsawa cikinta don neman kuri’a.
Wata karamar hukuma da za a sake zaben da ke da yawan kuri’a ita ce Michika. Akwai rumfunan zabe 3,464 da abin ya shafa.
Dan takarar PDP, Mista Zakariya Daudu ne ya lashe zaben Majalisar Wakilai ta Karamar Hukumar.
Karamar hukuma ta uku da ta fi yawan rumfunan zabe da abin ya shafa ita ce Lamurde.
Karamar hukumar ce ta fitar da ’yan takarar Mataimakan Gwamna biyu na PDP da APC, wato Seth Crowther da Farfesa Kaletapwa Farauta.
Sai dai ana tunanin Sanata Binani tana da hanyoyin lashe zabe da dama, musamman ganin yadda ta doke fitattun ’yan siyasa a zaben fid-dagwanin APC, ciki har da tsohon Gwamna Bindow da Malam Nuhu Ribadu da sauransu.
Haka nasarar da APC ta samu a zaben Shugaban Kasa ana ganin zai iya tasiri wajen taimaka wa Binani a zaben.
Shi kuma Gwamna Fintiri yana tare da goyon bayan dan takarar Shugaban Kasa na PDP Atiku Abubakar, wanda yake da matukar tasiri a siyasar Adamawa. A Jihar Kano za a sake zabe a wasu mazabu a kujerun ’yan Majalisar Wakilai biyu wato Fagge da Doguwa/Tudun Wada.
Baya ga wannan akwai sake zabe a kujerun ’yan Majalisar Dokoki ta Jihar da suka hada da kananan hukumomin Ajingi da Dambatta da Dawakin Tofa da Gezawa da Gwarzo da Makoda da Takai da Ungogo da Warawa da Gabasawa da Tudun Wada.
Sai dai kuma tun a ranar 4 ga Afrilu ’yan takarar Jam’iyyar NNPP su tara da suka hada da Aminu Sa’idu (Ungogo) da Isyaku Ali Danja (Gezawa) da Abdullahi Ali (Wudil) da Kabiru Getso Haruna (Gwarzo) da Mahmud Tajo (Gaya) da Abdullahi Iliyasu (Tudun Wada) da Ahmad Muhamamd (Dawakin Tofa) da Aminu Ibrahim (Dambatta) da Abdu Ibrahim Madari (Warawa) suka shigar da kara a Kotun Sauraren Kararrakin Zabe da ke zama a Miller Road,
Masu shigar da karar sun nemi kotun ta ba su damar da za su binciki kayayyakin da Hukumar INEC ta yi amfani da su a wajen zaben ’yan Majalisar Jihar da ka gudanaar a ranar 18 ga Maris 2023.
Masu sharhi kan al’amuran da ke faruwa sun ce tarihi ne zai maimaita kansa wato NNPP ce za ta lashe akasarin kujerun lura da cewa har yanzu akwai guguwar yayin jam’iyyar a jihar.
APC da Labour za su hade a Fagge don kada NNPP
Game da kujerar Majalisar Wakilai ta Fagge, duk da cewa sakamakon wasu mazabu da aka sanar dan takarar Jam’iyyar APC Sulaiman Gora ne ya zo na uku yayin da dan takarar Jam’iyyar LP Habungyare ke na biyu dan takarar NNPP Barista M.B. Shehu ke kan gaba.
Aminiya ta samu labarin cewa APC za ta tallafa wa LP wajen ganin NNPP ba ta kai gaci ba.
A Doguwa/Tudun Wada Hukumar INEC ta soke zaben mazabu 13 da ke Karamar Hukumar Tudun Wada saboda zarge-zargen da ake yi wa dan takarar APC Alhaji Alhassan Ado Doguwa na tayar da hankali da abubuwa da suka saba wa dokokin zabe.
Da farko har an bayyana Alhassan Ado Doguwa wanda shi ne Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai a matsayin wanda ya alshe zaben a kan abokin takararsa na Jam’iyyar NNPP, Iya Kwamanda Salisu Yusha’u, amma daga baya Hukumar INEC ta janye sanarwar bayan da Baturen Zaben ya ce ya bayyana sakamakon ne a yanayi na tursasawa amma akwai kurakurai a zaben.
Zargin da aka yi wa Doguwa ya kai ga Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ga kamawa da gurfanar da shi a gaban wata Kotun Majistare da ke jihar inda aka tuhume shi da laifin kisa da tayar da hankalin jama’a inda aka bayar da belinsa.
Kungiyoyi masu zaman kansu sun yi ta kiraye-kiraye a janye belin tare da sake gurfanar da shi gaban kotu. Aminiya ta lura hankali ya fi karkata kan zaben na Doguwa/ TudunWada.
Da yake jawabi kan karashen zabubbukan, Dokta Sa’idu Ahamd Dukawa malami a Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Bayero, Kano ya ce zabubbukan da za a gudanar gobe za su ja hankali lura da cewa fage ne da za gwada kwanji a tsakanin manyan jam’iyyun da ke hamayya da juna.
“Shi dama zaben cike gurbi yana jan hankali domin manyan jam’iyyun kowace na so ta ga ita ce ta yi nasara a zaben don ta fi ba wa ’yar uwarta tazara, ballantana a yanzu da Majalisar Wakilai ke cike da ’yan hamayya.
“Jam’iyya mai mulki za ta yi duk abin da za ta iya na takaita wa ’yan adawa lashe wadanan zabubbuka.
“Haka su ma jam’iyyun hamayya za su yi iya kokarinsu su ga sun lashe don haka zai zama akwai gasa mai tsanani.
“Don haka duk abin da yake na magudi a harkar a zabe za a iya yin sa.
“Babu mamaki cinikin kuri’u zai kankama sosai a zaben musamman yanzu da aka sassauta harkar samun kudi ga mutane.
“Kuma babu mamaki idan aka yi amfani da ’yan daba aka tarwatsa zaben ko aka fasa akwatu da sauran makamancin wannan.
“Idan muka yi la’akari da cewa sabuwar fasahar yin amfani da na’urar BBAS ta sa zai yi wahala a yi aringizon kuri’a a zaben don haka za a iya bin wata hanya wajen lalata kuri’un abokan hamayya,” in ji shi.
Dokta Dukawa ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su duba sosai don lalubo hanyoyin da za u toshe yiwuwar wadancan abubuwa da ya kissaaf a asama.
Ya ce, “Wajibi ne Hukumar INEC ta sa ido wajen ganin cewa ba a yi aringizon kuri’u ba, su kuma jami’an tsaro dole su sa ido ganin ba a yi amfani da ’yan daba wajen tayar da rikici a wajen zaben ba.
Haka hukumomin EFCC da ICPC su tsaya tsayin-daka don ganin ba a yi cinikin kuri’u ba. Idan kuma suka kama su tabbatar an yi hukunci a kai don ya zama darasi ga na baya.”
A goben ne dai tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato da Sanata Aliyu Wamakko da Gwamna Aminu Tambuwal za su san makomarsu ta zuwa Majalisar Dattawa ko a’a kamar yadda muka bayar da rahoto a makon jiya.
Haka tsohon Gwamna Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ma yana fuskantar irin wannan kalubale shi da wasu ’yan siyasa da dama a sassan kasar nan.