A gobe Asabar ce ake sa ran za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Manchester City da Manchester United a gasar Premier ta Ingila.
Wasan zai gudana ne a filin wasa na City da aka fi sani da Etihad Stadium da misalin karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya.
Masana kwallo suna ganin wasan zai yi zafi ganin kawo yanzu kulob din City wanda ya lashe gasar sau biyu a jere yana fuskantar kalubale kamar yadda kulob din Manchester United yake fuskantar kalubale.
Wannan shi ne wasa karo na 16 kuma saura wasa uku a kammala zagayen farko don haka duk kungiyar da ta yi sake aka doke ta to za a ba ta tazara.
Tuni manajojin kungiyoyin biyu wato Pep Guardiola na City da Solksjaer na United suka shirya tunkarar wannan wasa.