✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a rufe Bikin Wasanni na Jihar Kaduna

Agobe Asabar ake sa ran rufe bikin wasanni na Jihar Kaduna, wanda aka fara a ranar Lahadin da ta gabata. Da farko an shirya fara…

Agobe Asabar ake sa ran rufe bikin wasanni na Jihar Kaduna, wanda aka fara a ranar Lahadin da ta gabata.

Da farko an shirya fara bikin ne a ranar 27 zuwa 29 na Fabrairun bana, amma sai aka dage ranar fara bikin zuwa 1 ga Maris.

Masu shirya bikin sun ce bikin wassanin zai taimaka wajen bai wa ’yan wasan jihar horo don su samu damar shirya wa Gasar Wasannin ta Kasa Karo na 20 da  za a yi  a Jihar Edo daga ran 21 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu mai zuwa.

Bayanin haka na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Sakataren Ma’aikatar Wasanni ta Jihar Kaduna, Umar Kabiru Ibrahim da ya raba wa manema labarai.

Ya ce shugabannin kananan hukumomin jihar ne suka bukaci  a dage fara wasannin daga  watan Fabrairu zuwa Maris domin ba su damar shirya wa wasan da kyau.