✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a kece raini tsakanin Man United da Liberpool

A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu ne za a kece raini a tsakanin kulob din Manchester United da Liberpool a gasar rukunin Firimiya…

A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu ne za a kece raini a tsakanin kulob din Manchester United da Liberpool a gasar rukunin Firimiya ta Ingila.

Wasan shi ne wasa na 30 bayan da aka fara gasar ta bana. Kawo yanzu kulob din Manchester City ne ke saman teburin gasar da maki 78 sai Manchester United ke matsayi na biyu da maki 62 sai Liberpool ta uku mai maki 60 sai Tottenham ta hudu da maki 58.

 

Ke nan wasan goben zai kasance ne a tsakanin kungiyoyin da ke matsayi na biyu da na uku a gasar.  Idan United ta samu nasara  za ta ba Liberpool tazarar maki biyar ke nan amma idan Liberpool ce ta samu nasara za ta koma ta biyu a teburin gasar kuma za ta ba United tazarar maki daya.

Za a yi wasan ne a filin wasa na United da ake kira Old Trafford da misalin karfe daya da rabi na rana agogon Najeriya kuma ana sa ran gidajen kallon kwallon kafa za su cika makil da magoya baya don ganin yadda wasan zai kaya.