✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a gudanar da zaben shugabannin kungiyar ’yan Kasuwar Arewa

A gobe Asabar ne ake sa ran za a gudanar da zaben sabbin shugabannin kungiyar ’yan Kasuwar Arewa a garin Kaduna.  Shugaban kwamitin shirya zaben…

A gobe Asabar ne ake sa ran za a gudanar da zaben sabbin shugabannin kungiyar ’yan Kasuwar Arewa a garin Kaduna. 

Shugaban kwamitin shirya zaben kuma shugaban ’yan kasuwar Jihar Taraba, Alhaji Abdullahi Usman
Maikaka ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.
Ya ce ’yan takara da dama ne suka fito domin shiga zaben da za a gudanar gobe. Ya ce mutum uku ne daga kowace jiha daga yankin arewa da suka hada da shugaba da sakatare da ma’aji da kuma shugaba da sakatare na
kowace shiyya ta arewa ne za su yi wannan zabe.
Shugaban ya yi bayanin cewa sun yanke shawarar gudanar da zaben ne a wajen taron kungiyar da muka gudanar a ranar 10 ga watan Disambar bara.
Ya ce , “zamu gudanar da zaben ne domin a sami shugabannin da za su jogaranci ‘yan kasuwar arewa wajen yin magana da murya guda. Zaben shi ne zai bai wa ‘yan kasuwarmu ’yancinsu. Mu ‘yan kasuwa duk da cewa mune muka fi kowa yawa a kasar nan, amma ba ma samun taimakon da yakamata,”inji shi. Shugaban ya kara da cewa: “A kullum barayi suna tare ‘yan kasuwa a kan hanyoyin kasar nan, suna kwace masu dukiya, a kullum gobara tana cinyewa ‘yan kasuwarmu kayayyakinsu a kasuwanni, amma ba a taimaka masu. Saboda haka zamu hada kanmu mu zabi shugabanni da zasu kai kukanmu ga gwamnati domin a rika tallafa mana.
kungiyar tun da farko ta gudanar da zaben shugabannin wannan kungiyar na shiyyar Arewa–ta- Tsakiya da shiyyar Arewa-ta-Gabas da shiyar Arewa-maso-Yamma.
A karshe ya yi kira ga ‘yan kasuwar da su hada kansu, kuma su fito kwansu da kwarkwatarsu domin halartar zaben da za a gudanar tare da zaben shugabanni nagari.