✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a goge raini tsakanin Ja’e Academy da Jodano Academy a Kaduna

A gobe ne za fafata tsakanin kungiyar Ja’e Academy ta Kaduna da kungiyar Jodano Academy ta Jihar Kano a filin wasa na Kawo da ke…

A gobe ne za fafata tsakanin kungiyar Ja’e Academy ta Kaduna da kungiyar Jodano Academy ta Jihar Kano a filin wasa na Kawo da ke Kaduna.

Ita dai kungiyar Ja’e Academy ta je har Jihar Kano inda ta buga wasannin da dama ciki har da wasan da ta buga kungiyar Kano Pillars, sannan bayan ta dawo gida Kaduna sai Jodano Academy ta biyo ta har Kaduna domin sake buga wasan sada zumunta.

Da wakilin Aminiya yake zantawa da daya daga cikin mahukunta kungiyar Ja’e Academy, Dalhat Ja’e, ya tabbatar da cewa duk da cewa wasan sada zumunta ne, ba za su dauka da wasa ba “Saboda sada zumunta muka shirya wannan wasa, amma kuma wasan mai zafin gaske ne, kasancewa yanzu muka fara daga martabar wannan kungiya ta Ja’e Academy, ba za mu yi wasa ba da kowane irin wasa. Dole mu nema zura kwallaye da yawa, musamman kasancewa har gida suka biyo mu kuma dole mu nuna kwarewa. Bai kamata mu ba ‘yan kallonmu kunya ba.”