✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a fara gasar firimiya ta Ingila 2

A gobe Asabar 13 ga watan Agusta ne za a fara kakar wasa ta bana a Ingila da ake wa lakabi da English Premier League…

A gobe Asabar 13 ga watan Agusta ne za a fara kakar wasa ta bana a Ingila da ake wa lakabi da English Premier League (EPL). An canza wa gasar suna ne tun cikin shekarar 1992 watau kimanin shekaru 25 da suka wuce.  Gasar za ta gudana ne daga ranar 13 ga wannan wata zuwa 21 ga watan Mayun 2017.
kungiyar Leicester City ce ta kasance zakarar gasar a bara sannan kungiyoyin Burnely da Middesbroough da na Hull City ne suka hauro gasar daga rukunin ’yan dagaji.
A ranar farko, mai rike da kambun  Leicester City za ta fara wasa ne a waje da kungiyar Hull City  sannan Jose Mourinho zai jagoranci kungiyar Manchester United zuwa gidan kungiyar Bournemouth a filin wasa na Dean Court.
Sabon kocin Manchester City Pep Guardiola zai buga wasansa na farko ne da kungiyar Sunderland a filin wasa na Ettihad yayin da kulob din Chelsea za ta fara wasanta na farko ne a gida da kulob din West Ham United.  Arsenal kuma za ta kece raini ne da Liberpool a filin wasa na Emirates.
Manchester United da ke karkashin horarwar Jose Mourinho za ta hadu da kulob din Chelsea ne a ranar 22 ga watan Oktoba sannan a mako na hudu ne za a fafata a tsakanin Manchester City da ke karkashin horarwar Pep Guadiola da kuma Manchester United da ke karkashin kulawar Mourinho.  Wasan zai gudana ne a ranar 10 ga watan Satumbar wannan shekara.