A gobe Asabar ne ake sa ran za a fara gasar cin kofin matasa na Afirka da ake wa lakabi da African Nations Championship (CHAN). Gasar za ta gudana ne a kasar Ruwanda. Haka kuma gasa ce da ’yan kwallon gida suke fafatawa a cikinta. Kenan duk dan kwallon da ke yin kwallo a waje ba ya cikin wadanda za su yi gasar.
kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta fafata ne a rukunin C tare da Tunisiya da Nijar da kuma Guinea. Sai dai Najeriya za ta fara wasanta na farko ne a ranar Litinin inda za ta kece raini da Nijar a filin wasa na Kigali.
Idan za a tuna, dan kwallon Najeriya Gbolaham Salami ya fice daga ’yan kwallon da za su fafata a gasar ce inda ya tafi Turai don sanya hannu a wani kulob da ba a ambata ba yayin da Oghenekaro Etebo kuma wanda ya lashe kyautar Hukumar CAF ta matashin dan kwallon da ya fi kokari aa kakar wasan 2015 ba a gayyace shi don tafiya gasar ba.
Sai dai dan kwallon baya a kulob din Super Eagles Chris Madaki ya bayar da tabbacin za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun lashe wa Najeriya kofin.
Yanzu dai kulob din ya dogara ne da dan kwallon gaba a kulob din Sunshine Stars na Akure Tunde Adeniji da kuma Cleber Chisom da ake wa lakabi da “Kolanut Boy” wajen zura kwallo a raga a gasar. Kuma dukkan ’yan kwallon ba su dade da farfadowa daga raunin da suka samu ba.
Gobe za a fara gasar cin kofin matasa na Afirka(1)
A gobe Asabar ne ake sa ran za a fara gasar cin kofin matasa na Afirka da ake wa lakabi da African Nations Championship (CHAN). …