✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Super Eagles za ta sauka a Zambiya

Ga dukkan alamu sai gobe Asabar ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta sauka a kasar Zambiya a shirye-shiryen tunkarar wasan neman gurbin…

Ga dukkan alamu sai gobe Asabar ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta sauka a kasar Zambiya a shirye-shiryen tunkarar wasan neman gurbin zuwa gasar cin Kofin Duniya.
Tun a ranar Talatar da ta wuce ne daukacin ’yan wasan Super Eagles da jami’ansu kimanin 22 suka hallara a Abuja inda suka yi atisaye a karkashin sabon koci Grenot Rohr.  Kamar yadda kocin ya sanar, ’yan kwallon za su ci gaba da samun horo a Babban Filin Wasa na kasa da ke Abuja har zuwa yau Juma’a kafin su tashi zuwa Zambiya a gobe Asabar da sassafe.
Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar Super Eagles Toyin Ibitoye ya sanar da cewa ’yan wasan suna cikin koshin lafiya kuma sun shirya tsaf domin tunkarar wasansu da Zambiya.  Ya ce yana fatan ’yan kwallon za su ba marada kunya wajen doke Zambiya a wasan da zai gudana a jibi Lahadi.  Wasan dai zai gudana ne a filin wasa na Nwanwasa da ke Ndola na kasar Zambiya da misalin karfe daya da rabi na rana agogon Najeriya.
Najeriya dai tana rukunin B ne inda za ta kece raini da kasashen Kamaru da Aljeriya da kuma Zambiya.  Duk kasar da ta kasance ta farko a rukunin ce za ta haye zuwa gasar cin Kofin Duniya da za a yi a Rasha a shekarar 2018.
Sau biyu a jere Najeriya ta kasa halartar gasar cin Kofin Duniya da ya gudana a kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2010 da kuma wacce ta gudana a Brazil a shekarar 2014.  Idan ta kasa hayewa zuwa gasar da za ta gudana a Rasha a 2018 zai zama sau uku ke nan a jere.
Masana harkar kwallo suna ganin da wuya Super Eagles ta tsinana wani abu a wasannin neman hayewa gasar ganin ta fada rukunin da ake ganin ya fi kowane rukuni zafi da kuma yadda Hukumar NFF ta fara korafi a kan rashin isassun kudi don tunkarar gasar al’amarin da ake ganin tun ba a ce ko’ina ba har an fara samun cikas.