✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe sabon kocin Eagles zai fara wasansa na farko

A gobe Asabar 3 ga wannan wata da muke ciki ne za a yi wasan neman hayewa gasar cin kofin Afirka inda za a kara…

A gobe Asabar 3 ga wannan wata da muke ciki ne za a yi wasan neman hayewa gasar cin kofin Afirka inda za a kara a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da takwararta ta Tanzaniya.  Wasan zai gudana ne a filin wasa na garin Uyo da ke Jihar Akwa Ibom da misalin karfe biyar na yamma agogon Najeriya.  Wannan shi zai kasance wasan farko ga sabon kocin Eagles, dan asalin Jamus Grenot Rohr tun bayan da ya kulla yarjejeniya da hukumar NFF a watan jiya.
Tuni kocin ya gayyato zaratan ’yan kwallo daga ciki da wajen Najeriya da suka hada da Kyaftin John Mikel Obi da Brown Ideye da bictor Osimhen da Musa Mohammed da Jami’u Alimi da mai tsaron gida Emmanuel Daniel da sauransu.
Kodayake wasan zai kasance ne a matsayin  je-ka-na-yi ka, don ko kungiyar Eagles ta samu nasara a kan Tanzaniya ba za ta halarci gasar cin kofin Afirka ba, don tuni kasar Masar ta kasance jagora a rukunin bayan ta doke Najeriya da ci 2-0 a watan Maris din wannan shekara a can kasar Masar.
Kawo yanzu Masar ce ka kan gaba a teburin da ke rukunin G da maki 10 sai Najeriya mai maki 2 sai Tanzaniya mai maki daya sai kuma Chad da ba ta da maki ko daya.
Kenan idan Najeriya ta doke Tanzaniya a gobe, za ta hada maki 5 kuma ta kasance ta biyu inda watakila ta haye a matsayin kasar da ta yi kwazo amma ba ta samu damar hayewa gasar ba tun farko.
Idan za a tuna Chadi dai ta janye daga gasar ce saboda matsalar rashin kudi al’amarin da ya sa aka zaftare wa duk kasashen da ke rukunin makin da suka samu a kan Chadi kamar yadda dokar hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta tanadar.  Dokar ta nuna duk kasar da ta janye a lokacin da gasar ke gudana, to za a zaftare makin da aka samu a kanta daga adadin makin da kowace kasa ta samu.
Sai dai ya zuwa makon jiya an samu rade-radin cewa kasar Chadi ta amince ta cigaba da fafatawa a gasar da watakila hakan ya ba  Najeriya dama ta samu hayewa gasar cin kofin Afirka da zai gudana a shekara mai zuwa a Gabon.
Za a fara gasar cin kofin Afirka a Gabon ne daga ranar 14 ga Janairu zuwa 5 ga watan Fabrairun, 2017.
Idan Najeriya ba ta laharci gasar ba, wannan zai kasance shi ne karo na biyu a jere.  Ba ta halarci gasar da ta gudana a shekarar 2015 a Ekuatorial Guinea ba.