A cigaba da gasar cin kwallon kafa na duniya na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) a Chile, a gobe Asabar 24 ga wannan wata da muke ciki ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da aka fi sani da Golden Eaglets za ta hadu da Kuroshiya a wasa zagaye na biyu.
kungiyar kwallon kafa ta Eaglets dai ta lashe wasanninta biyu al’amarin da ya sa yanzu ta haura zuwa zagaye na biyu a gasar inda za ta kara da Kuroshiyan a gobe.
Najeriya ta doke Amurka ne da ci 2-0 a wasan farko, yayin da ta yi kaca-kacal da mai masaukin baki Chile a ranar Talatar da ta wuce da ci 5-1. Idan Najeriya ta samu nasara a wasanta na gobe, za ta haye matakin kwata-fainal kenan a gasar.
Idan za a tuna Eaglets ce take rike da kofin a halin yanzu bayan ta lashe gasar da ta gudana a Hadaddaiyar Daular Larabawa (UAE) a shekarar 2013. Sannan Najeriya ta lashe kofin har sau hudu a tarihin gasar.
Tuni kocin kungiyar Emmanuel Amunike ya hori ’yan kwallon da su yi kokarin ganin sun samu nasara a wasan gobe, don ganin sun cigaba da haskakawa a gasar.
A karshen makon jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan kwallon da su yi kokarin lashe kofin a karo na biyar don ganin sun daukaka martabar Najeriya a idon duniya.