✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Buhari zai san abokin karawarsa

A gobe Asabar ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai san babban abokin karawarsa a zaben Shugaban Kasa da za a gudanar a badi.…

A gobe Asabar ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai san babban abokin karawarsa a zaben Shugaban Kasa da za a gudanar a badi.

A goben ne ake sa ran babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta gudanar da Babban Taronta don fitar da wanda zai rike mata tuta a zaben na badi. Babban Taron zai gudana ne a birnin Fatakwal fadar Jihar Ribas da ke Kudu maso Kudu, inda wakilan jam’iyya za su zabi wanda zai tsaya wa jam’iyyar takarar Shugaban Kasa da zai fatata da Shugaba Buhari.

Yadda zaben PDP zai kasance

Jam’iyyar PDP tana da masu son tsaya mata takarar Shugaban Kasa guda 12 da suka hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa da Gwamnan Jihar Gombe mai barin gado na Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo da tsohon Gwamnan Jihar Filato da Sanata Jonah Jang da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido.

Sauran su ne tsohon Sanata Dokta Datti Baba-Ahmed, da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa da Sanata Dabid Mark da kuma tsohon Minitan Ayyuka na Musamman, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki.

Dukan ’yan takarar sun nace kai-da-fata cewa ba za su janye daga takarar ba, domin kowannensu yana ganin shi ya fi cancanta ya zama wanda zai rike tutar Jam’iyyar PDP don fuskantar Shugaba Buhari a zaben na badi.

Kokarin da Shugaban Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP ta Kasa, Sanata Walid Jibrin ya yi domin fitar da dan takarar Shugaban Kasa ta hanyar sulhu, ko a rage yawansu ya ci tura.

Shugaban Matasan Jam’iyyar PDP a Jihar Borno, Umar Sanda, ya bayyana wa Aminiya cewa hakika idan ’yan takarar 12 ba su hada kansu sun fitar da gwarzo guda daya daga cikinsu ba, to wanki hula zai jam’iyyar ga dare.

“Zaben da za a yi na Shugaban Kasa a badi ba kamar wanda aka yi a shekarar 2015 ba ne, inda a wancan lokaci Shugaba Buhari wanda dan Arewa ne ya kalubalanci Goodluck Jonathan mai mulki kuma dan Kudu. Amma a wannan lokaci duk ’yan Arewa ne a fagen daga, kuma kowa ya san irin farin jinin da Shugaba Buhari yake da shi, don haka ya zama tilas ga Jam’iyyar PDP ta fitar da gwarzo mai tagomashi wanda ’yan Najeriya za su amince da shi,” inji Sanda.

Wani mai sharhi a kan al’amuran siyasa a Jihar Kano, Aminu Danmalam, cewa ya yi sai wakilan Jam’iyyar PDP sun yi da gaske sun ajiye maganar kabilanci da son abin duniya kafin su cimma burinsu na kwace mulki daga Shugaba Buhari.

Ya ce: “Dole dai su nemo dan takarar da zai iya bugun kirjinsa ya ce shi ma mai gaskiya ne kamar Shugaba Buhari. Kuma dole ne dan takarar nasu ya gamsar da miliyoyin ’yan Najeriya da za su kada kuri’a cewa shi ma babu daudar cin hanci da rashawa a jikinsa. Haka kuma dole ne su zabo wanda zai gamsar da ’yan Najeriya cewa zai gyara tattalin arzikin kasa kuma zai iya kawo zaman lafiya a sassa daban-daban na kasar nan, kuma zai iya hada kan ’yan Najeriya.”

Shugaban Jam’iyyar NDLP ta Kasa, Alhaji Umaru Mohammed Maizabura, cewa ya yi akwai babban aiki a gaban ’ya’yan Jam’iyyar PDP. “Ai ’ya’yan Jam’iyyar PDP sun harbi kansu a kafafunsu tun ba a je ko’ina ba,” inji shi.

“Kuma hakika ina ganin ba su yi shirin fuskantar Shugaba Buhari a fagen zabe ba saboda wannan irin takun-saka da suke yi,” inji shi.

“Yaya za a yi su fitar da dan takara guda daya daga cikin ’yan takara 12? Ai wannan ba karamin aiki ba ne. Ina tabbatar maka daga an kammala zaben fitar da gwani, mafi yawancinsu za su bar jam’iyyar,” inji shi.

Maizabura wanda ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta NDLP tuni ta tsayar da Barista Libasan daga yankin Kudu a matsayin dan takararta na Shugaban Kasa, ya ce ya san Shugaba Buhari ne zai kai ga nasara. Ya ce“Kowa a kasar nan ya san cewa ina da jam’iyyata kuma na yi takarar Shugaban Kasa ba sau daya ko sau biyu ba. Amma a wannan karon na janye domin in mara wa Shugaba Buhari baya.”

Da wakilinmu ya tambaye shi ko wane ne yake ganin zai iya ja da Buhari sosai a cikin ’yan takarar PDP? Ya ce: “A ganina idan suka ba Atiku Abubakar tikitin takarar, to zai iya daga wa APC hankali ne kawai, amma ba wai zai ci zabe ba; za a fafata sosai saboda ya dade yana kamfe a yankuna da dama na kasar nan. Amma ina tabbatar maka cewa idan suka bai wa wani dan takarar daban, to jam’iyyarsu ta PDP ba za a ji duriyarta ba bayan sun bar birnin Fatakwal domin kowane dan takara zai kama gabansa ne kawai.”

Ana bita-da-kulli kafin zaben

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa tuni masu fada-a-ji a Jam’iyyyar PDP, kamar gwamnoni irin su Nyewom Wike na Jihar Ribas da Ayo Fayose na Jihar Ekiti da Gwamna Seriake Dickson na Jihar Bayalsa da Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom da kuma Darius Ishaku na Jihar Taraba da sauransu, suna kokarin daukar dan takararsu daga cikin gwamnonin jam’iyyar daga yankin Arewa.

A yanzu dai gwamnonin PDP da ke takara su biyu ne- Ibrahim Dankwambo daga Jihar Gombe da Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato.

Tuni aka fara zargin gwamnonin jam’iyyar daga yankin Kudu cewa sun kai taron ne Fatakwal domin su samu damar cin karensu babu babbaka.

Mako biyu da suka gabata ma an yamutsa fuska a tsakanin shugabannin jam’iyyar game da garin da ya dace a gudanar da Babban Taron Jam’iyyar da zai zabi gwanin jam’iyyar.

Shugabannin Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP a karkashin Sanata Walid Jibrin ba su gamsu da zabar Fatakwal ba; amma Shugaban Jam’iyyar ta Kasa Cif Uche Secondus, wanda ake ganin dan gaban goshin Gwamna Wike ne, ya nuna goyon bayansa a kan cewa sun fi so a tafi Fatakwal a yi taron.

Duk da cewa Gwamna Dankwambo ya dade da nuna sha’awarsa ta neman takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, masu fashin baki suna ganin hankalin shugabannin jam’iyyar ya fi karkata kan Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal.

A shekaranjiya Laraba, Gwamna AminuTambuwal ya yi wata ganawar sirri da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a Otta da ke Jihar Ogun.

Gwamna Tambuwal ya bayyana wa manema labarai cewa hakika yana sa ran samun tikitin PDP domin ya tunkari Shugaba Buhari a zaben mai zuwa.

“Najeriya tana bukatar Shugaban da zai hada kan al’umma kuma ina ganin ina da hazakar da zan yi hakan,” inji shi.

Sai dai mutanen Arewa ta Tsakiya suna ta kokarin ganin an fitar da dan takarar PDP daga cikinsu.

’Yan takarar da suka fito daga shiyyar sun hada da Sanata Bukola Saraki da Sanata Dabid Mark da kuma Sanata Jonah Jang. Wani dan jam’iyyar da ba ya so a bayyana sunansa ya shaida wa Aminiya cewa a karshe babu mamaki Sanata Jang da Sanata Dabid Mark su janye daga takarar domin su mara wa Sanata Bukola Saraki baya.

“Burin mutanen yankin Tsakiyar Najeriya (Midil Belt) shi ne su samu Shugaban Kasa; to a halin da ake ciki zai yi wuya Kirista ya samu galaba a zaben 2019, don haka ne mutanen yankin suke ganin Sanata Saraki wanda ya fito daga Jihar Kwara zai iya cin nasara,” inji shi.

A farkon makon nan tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana wa jaridar Daily Trust cewa kai taron Jihar Ribas ba zai canja komai ba.

“Ni ina ganin idan aka bai wa wakilan jam’iyya dama su zabi wanda suke so, to komai zai tafi daidai,” inji shi.

Shi ma Sanata Kwankwaso ya bayana cewa yana da yakinin cewa shi ne zai kai ga nasara a zaben fid da gwanin, inda ya ce shi ne kadai zai iya kayar da Shugaba Buhari a zaben Shugaban Kasar.

A wata ziyara da ya kai jiharsa ta Kano a makon jiya gabata, Sanata Kwankwaso bayyana cewa Jihar Kano tana wakilai masu zabe fiye da kowace jiha a kasar nan.

“Haka kuma muna da magoya baya a kowane yanki na kasar nan,” inji shi.

Akwai dai jam’iyyun siyasa sama da 90 a Najeriya, kuma da yawa sun bayyana cewa za su tsayar da ’yan takara a matakai daban-daban har da na Shugaban Kasa, ko kai- tsaye ko ta hanyar hadin gwiwa da wasu jam’iyyun.

Sai dai ’yan Najeriya, ciki har da ’yan siyasa da masu fashin baki kan al’amuran siyasa a sassan na duniya suna ganin cewar dan takarar da zai fafata da Shugaba Buhari zai fito ne daga Jam’iyyar PDP.

Ita dai jam’iyya mai mulki wato APC tun ranar Asabar da ta gabata ce ta gabatar da nata zaben fid da dan takarar Shugaban Kasar wanda Shugaba Buhari kadai ne ya tsaya.

Zaben dai an gudanar da shi ne a rumfunan jefa kuri’a sama da 9000 a kananan hukumomi 776 da ke jihohi 36 d Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.

Shugaba Buhari ya samu miliyoyin kuri’a a zaben fid da gwani da aka yi a jihohin, inda a Jihar Kano ya samu kuri’a miliyan biyu da dubu 900d; sai Bauchi miliyan daya da dubu 200; a Taraba ya samu kuri’a dubu 800, Adamawa miliyan biyu, Benuwai dubu 259 da 130; Imo, dubu 697 da 532; sai Zamfara, dubu 247 da 847; Katsina kuma dubu 802 da 819 da sauransu.

Shugaban Jam’iyar APC ta Kasa Kwamared Adams Oshiomhole ya bayyana cewa suna da magoya baya miliyan 15 da dubu 156, wadanda za su yi jefa wa jam’iyyar kuri’a a zaben badi, ban da magoya bayan wasu jam’iyyu da za su kada wa Shugaba Buhari kuri’a.

Mai bai wa Shugaba Buhari, Shawara kan Harkar Labarai, Malam Garba Shehu ya ce zaben fida gwani na Shugaban Kasa da aka yi wa Shugaba Buhari  a makon jiya alama ce ta samun nasararsa  a nan gaba.

Don haka ana ganin duk wanda zai ja da shi daga Jam’iyyar PDP sai ya shirya sosai.