Dukiyoyin miliyoyin Nairori sun salwanta bayan wasu tankoki dauke mai lita 33,000 sun yi hatsari a kan gadar Otedola dake kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 2:30 na daren ranar Asabar a gadar Otedola dake kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.
To sai dai ba a sami asarar rai ko daya ba in banda wasu da suka sami raunuka.
Rahotanni dai sun nuna cewa yawancin wadanda suka samu raunukan sun samu ne bayan faduwar tankar inda suka je da jarkoki domin dibar ganima.
Mutanen dai sun yi ta cika jarkokin suna guduwa da su a baro.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Legas, Muyiwa Adejobi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tankokin mai guda biyu hatsarin ya rutsa da su.
Ya ce hatsarin ya kuma shafi wata kwatena a kan gadar dake kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Muyiwa ya kara da cewa, “Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas ya ziyarci wurin da hatsarin ya faru domin duba barnar da lamarin ya yi da kuma taimakawa wajen rage cunkoson ababen hawa a waurin.
“Ya taimakawa jami’an tsaro na Hukumar Kiyaye Hadurra, NSCDC, hukumomi bayar da agajin gaggawa na kasa da ta jihar Legas, da na kiyaye gobara inda suka yi ta aiki tukuru wajen ceto tun karfe 2:30 na dare.
“Ba a sami asarar rai ko da daya ba kuma ana ta kokarin ganin ba a sami cunkoson ababen hawa a hanyar,” inji kakakin.
Ya ce binciken farko-farko ya gano cewa hatsarin ya faru ne sakamakon wani direban kwantena da motar ta kwace masa ya kuma afkawa tankokin dake dauke da man inda nan take kuma suka kama da wuta.