✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar gas: Gwamna El-Rufai ya hana dura gas a cikin jama’a

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya bada umarnin rufe shagunandura gas da sayar shi a tsakiyar gidajen jama’a a Kaduna babban birnin jihar. Gwamnan…

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya bada umarnin rufe shagunandura gas da sayar shi a tsakiyar gidajen jama’a a Kaduna babban birnin jihar.

Gwamnan ya bada umarnin ne bayan ya ziyarci inda tukwanen gas suka fashe suka yi sanadiyar mutuwar mutum shida a ranar Asabar da ta wuce a Unguwar Sabon Tasha a Kaduna. Cikin wadanda suka rasu akwai Farfesa Simon Mallam na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wanda ya je aski a wani shago da ke kusa da inda ake sayar da gas din.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Mista  Samuel Aruwan ta ce umarnin ya nuna duk wani shago da ake durawa da sayar da gas a kusa da inda abin ya faru za a rufe shi.

Har ila yau an kuma bukaci ma’aikatun da alhakin kare rayukan jama’a ya rataya a kansu su bincika suka ga an tabbatar da bin wannan umarni da aka bayar. An kuma bukaci ma’aikatun da su fito da tsarin yadda za a canja wa masu irin wannan sana’a wajen zama maimaikon zama cikin jama’a da hakan ke da babban hadari.

Idan ba a manta ba, fashewar gas ta yi matukar tayar da hankalin jama’a a garin Sabo da Boro saboda gobarar da ta tashi a wurin inda ta lakume dukiyayi sama da Naira miliyan 16 , inji ’yan sanda.