✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta yi barna a kasuwar Yola da Lafiya

A safiyar Litinin ne gobara ta tashi a kasuwar garin Yola wanda ta cinye dukiya  mai yawa.Rahotanni sun bayyana cewa ba a taba samun irin…

A safiyar Litinin ne gobara ta tashi a kasuwar garin Yola wanda ta cinye dukiya  mai yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa ba a taba samun irin wannan gobarar ba a tarihin Jihar Adamawa wanda ta cinye kusan kashi 90 ciikin 100 na kayayyakin da ke kasuwar.
Kamar yadda wani wanda gobarar ta tashi a gabansa ya ce, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:30 na dare. Ya ce “an yi iya kokari kashe wutar, amma hakan ya ci tura sakamakon rashin hanya mai kyau a cikin kasuwar.”
Har ila yau, Malam Babayola wanda ke da shago a cikin kasuwar ya ce shima shagonsa ya kone kurumus. “Gobarar ta tashi ne a tsakiyar kasuwar, kuma mutane sun yi kokarin su shiga su kai agaji, amma matakan tsaro sun hana a shiga domin kada a samu asarar rayuka da kuma sata,” inji shi.
A wani labarin mai kama da wannan kuma, gobara ta tashi a wani bangaren shaguna da ke sabuwar babbar kasuwar zamani da ke garin Lafiya da ke Jihar Nasarawa, inda ta cinye dukiyoyin miliyoyin naira.
Aminiya ta ziyarci kasuwar, inda ta gana da wani daga cikin wadanda lamarin ya shafi shagunansa biyu, Alhaji Hudu Ndagi, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan sun tashi daga kasuwar sun rufe shagunansu sun koma gida. Ya ce: “bayan mun tashi ina gida sai wani abokina ya kirani ta waya ya shaida mini cewa gobara ta tashi a shagona. Da jin haka sai na shiga motata na tafi kasuwar, inda na tarar da jama’a da dama ciki har da jami’an kwana-kwana suna kokarin kashe gobarar. Amma da yake lamarin ya faru da dadadare ne bayan galibin ’yan kasuwa sun tashi ya sa gobarar ta kone kusan duka kayayyakin da ke wadannan shaguna kafin a shawo kanta. Bayan an kashe wutar ne sai na shiga daya daga cikin shagunana don shagunana biyu ne gobarar ta cinye. Da na shiga sai na tarar gobarar ta kone duka kayayyakin shagon. Da na shiga na biyun sai shi ma na tarar wutar ta cinye kayayyakin, inda kananan kayayyaki da suka rage kuma ruwa da aka yi amfani dashi wajen kashe gobarar ya lalata su. Ina sayar da zare ne kamar zaren ulu da saka da na dinki da dai sauransu,” inji shi.
Har ila yau, ya ci gaba da cewa “ shagunan da ke kusa da nawa ana sayar da takalma ne da kayayyakin yara da sauransu. Kuma gobarar ta faru ne bayan na dawo daga Legas, inda na je na sayo wadannan kayayyaki da kudinsu ya kai fiye da naira miliyan biyu.”
dan kasuwan ya kara da cewa bayan an kashe gobarar ne suka fahimci cewa wutar ta faro ne daga daya daga cikin shagunan wani mutumin da ya tafi Kudu don yin bikin Kirsimeti.
Kamar yadda ya bayyana mutumin ya manta ne bai kashe Stabiliza da ke shagonsa ba, inda da aka kawo wutar ta lantarki sai ta kama da wuta don wutar ta yi mata yawa.
Daga nan sai ya bukaci gwamnati da masu hannu da shuni su tallafa musu don a cewarsa a halin yanzu sun rasa duka dukiyoyinsu a sakamakon gobarar.
Kimanin shaguna takwas ne gobarar ta kone kurmus kuma dukansu manyan shaguna ne cike da kayayyakin miliyoyin naira.
Shi ma a nasa bangaren Shugaban Kasuwar Alhaji Muhammad Nuruddeen ya jajantawa wadanda lamarin ya shafa, inda ya bukace su su dauki lamarin a matsayin kaddara ce daga Ubangiji.
Har ila yau, ya bukaci gwamnati ta kawo musu dauki ta hanyan tallafa musu don ba su damar sake gina sabuwar rayuwa. Daga nan sai ya yi kira ta musamman ga ’yan kasuwar baki daya musamman wadanda ke mallakar shaguna wadanda aka fi sani da Attachment su rika tabbatar da duka kayayyakin lantarki suna kashe kafin su bar shagunansu zuwa gida don guje wa aukuwar irin wannan lamarin nan gaba.
A karshe ya yi kira ga gwamnatin jihar da sauran kungiyoyi su taimaka wa wadanda lamarin ya shafa don rage musu asara.