✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a Kotun Kolin Najeriya

A safiyar Litinin gobara ta tashi a Kotun Koli

An samu gobara a Kotun Kolin Najeriya da ke Abuja a safiyar Litinin.

Gobarar ta babbake ofisoshin wasu alkalai uku, a yayin da ma’aikata suka tsere domin kubutar da rayuwarsu.

Zuwa yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma majiyarmu ta ce jami’an hukumar kashe gobara sun isa harabar kotun.

Wannan na daga cikin gobarar da aka samu a manyan cibiyoyin gwamnati a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A watan Mayun 2023 gobara ta lakume wani yanki na barikin sojojin sama da ke Abuja.

A cikin watan ne aka yi gobara a ginin Hukumar Akwatin Gidan Waya (NIPOST) a Abujar.

A watan Afrilu Ofishin Akanta-Janar na Kasa (AGF) ya yi gobara.