✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara Ta Tashi A Dakin Kwanan Dalibai Mata A Jami’ar Yobe

An kwantar dalibai takwas a asibiti sakamakon gobara a dakin kwanan dalibai mata

An kwantar dalibai takwas a asibiti sakamakon gobara a dakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Yobe da ke Damaturu.

Gobarar da ta tashi ne daga wata tukunyar din gas din girke inda ta kone dakin kwanan daliban misalin karfe 7 na daren ranar Talata.

Hukumomin jami’ar jihar sun ce yan kwana-kwanan jami’ar jihar da na hukumar kashe gobara ta jihar ne suka shawo kan gobarar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Abdulmumini Kolo Gulani ta ce an kwashe dukkan daliban, ba sa samu asarar rai ba.

Ya kara da cewa ba a san musabbabin faruwar lamarin ba, amma hukmomin jami’ar na aiki tare da sashin tsaro da kashe gobara na jami’ar domin gano musabbabin faruwar lamarin. 

Gwamna Mai Mala Buni na jihar ya jajantawa masu jami’ar da kuma daliban amma ya yi hamdala saboda ba a rasa rai ba.

Ya kuma umurci hukumar agajin gaggawa ta jihar da ta samar da abinci, tufafi, da shimfidu, a yayin da gwamnatin za ta sama wa daliban wani wurin kwanan.

Gwamnan ya bukaci daliban da al’ummar jihar da su yi taka tsantsan tare da kauce wa abubuwan da za su iya haddasa gobara.