✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kone wani sashen gidan wuta na Dan-Agundi dake Kano

Wata gobara ta tashi a tashar wutar lantarki ta Dan-Agundi dake Kano a ranar Litinin. Gobarar, wacce ta tashi da misalin karfe 11 na safe,…

Wata gobara ta tashi a tashar wutar lantarki ta Dan-Agundi dake Kano a ranar Litinin.

Gobarar, wacce ta tashi da misalin karfe 11 na safe, ta yi sanadiyyar konewar daya daga cikin injinan rarraba wuta da ke tashar kafin jami’an kwana-kwana su yi nasarar kashe ta.

“Lokacin da gobarar ta tashi, ma’aikatan tashar sun kashe dukkan na’urorin wutar da ke gidan cikin gaggawa kafin daga bisani ’yan kwana-kwana su zo su kashe wutar”, inji wani ganau a wajen da wutar ta kama.

Daya daga cikin injinan rarraba wutar da gobarar ta shafa

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce na’urar rarraba wutar lantarki guda daya ce lamarin ya shafa.

Mai Magana da yawun hukumar, CFO Sa’id Muhammd Ibrahim ya ce na’urar wata babba ce wadda ke sada wasu bangarorin na birnin Kano da wutar lantarki.

“Jami’an hukumar mu sun isa wurin da misalin karfe 11 na safe kuma sun sami nasara kashe wutar wacce ta kama wata na’urar taransifoma mai karfin MVA 15. Yanzu haka muna nan muna bincike don gano musabbabi wutar da kuma irin girman barnar da ta yi”, in ji kakakin hukumar.

A nasa bangaren kuwa Kamfanin rarraba wutar lantarki na shiyyar Kano (KEDCO) tab akin kakakin, Ibrahim Sani Shawai ya yi kira ga mutane da kada su tsorata duk da iftila’in gobarar, yana mai cewa suna yin duk mai yuwuwa wajen shawo ka lamarin.

Ya ce, “Daya daga cikin na’urorinmu ce karfin wuta ya yi mata yawa wanda hakan yayi sanadiyyar kamawarta da wuta. Hakan kuma ya shafi uku daga cikin hanyoyin rarraba wutar”.

A sakamakon hakan, kamfanin ya ce mazauna unguwannin Kofar Na’isa, Kofar Nasarawa, titin Ibrahim Taiwo, anguwannin cikin birni, kasuwar Yan Kifi ta kusa da titin gidan ajiye namun daji da kuma Gandun Albasa za su fuskanci karancin wuta kafin lokacin da kamfanin zai shawo kan matsalar.