Akalla shaguna 14 ne suka kone kurmus bayan watan gobara da aka yi a kasuwar Ijesa da ke Surulere a Jihar Legas.
Gobarar ta kuma kone karin wasu shagunan guda 48 sama-sama, da kuma akalla dakunan kwana 24.
- Ramadan: Ba ma bin ganin watan Saudiyya —Sarkin Musulmi
- Tsoron iyayenmu na hana maza neman aurenmu —’Yan matan barikin soja
- An samu gobara sau 767 a Zamfara a 2020
- APC ta lashe zaben kananan hukumomin Kano
Wutar dai wadda ta fara ci da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Asabar ta shafe kimanin sa’o’i hudu tana barnar, kafin daga bisani ’yan kwana-kwana su samu nasarar kashe ta.
Ko da yake ba a samu asarar rai ko daya ba in banda raunuka, jami’an bayar da agajin gaggawa sun tabbatar da cewa ta wutar ta tashi ne daga wani daki da aka mayar da shi shago.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), takwarar ta jihar Legas (LASEMA), da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Jihar ne suka yi taron dangi wajen kashe wutar.
Jami’in Hukumar NEMA mai kula da shiyyar Legas, Ibrahim Farinloye ya ce gobarar ta samo asali ne daga fashewar wata tukunyar gas da ake girki da ita.
Ya ce jami’ansu sun fuskanci matsalar karancin ruwan kashe gobarar, ta yadda sai da suka yi tafiyar tsawon wasu kilomitoci kafin su samo ruwan.
Kazalika, Mukaddashin Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, Misis Margaret Adeseye ta ce tuni suka dukufa da bincike domin gano musabbabin gobarar.
Ta kuma yi kira ga jama’a kan su yi taka-tsan-tsan wajen amfani da kayan wuta tare da tabbatar da cewa kwararrun masu gyara ne kadai suke gayyata idan kayan sun samu matsala.