Akalla mutum 55 ne suka rasu sakamakon gobarar tankar dakon mai a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar a ranar Lahadi da ta gabata.
Hukumomin kasar sun ce akwai kuma wadansu mutum 30 da suka samu munanan raunuka a hadarin.
Gidan Rediyon BBC ya ruwaito Babban Daraktan Hukumar Kare Hakkin Fararen Hula na kasar, Kanar Boubacar Bako yana cewa lamarin ya faru ne a cikin dare kusa da filin jirgin saman Yamai.
Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne bayan mutane sun yi dafifi a inda tankar ta fadi a kokarinsu na kwasar mai abin da ya haddasa ta yi bindiga.
Firayi Ministan kasar Nijar da wadansu ministocinsa sun ziyarci inda aka samu bala’in, inda daga bisani suka wuce asibiti domin duba wadanda suka ji rauni.