An tabbatar da mutuwar mutane biyu a gobar da ta tashi a wani sashe na gidan tsohon Gwamnan Jihar Oyo, marigayi Otunba Christopher Adebayo Alao Akala da ke garin Ogbomoso.
Wata majiya ta kusa da tsohon gwamnan ta shaida wa Aminiya cewa gobarar ta tashi ne a ranar litinin da safe a sashen ‘boys quarters’ na gidan da ke unguwar Randa a garin na Ogbomoso.
Majiyar ta ce binciken farko ya tabbatar da cewa fashewar tukunyar girki da gas ce ta haifar da tashin gobarar da ta yi sanadin mutuwar wadannan mutane biyu da ke cikin dakunansu kafin makwabta su kai dauki da hadin kan jami’an kashe gobara da suka yi nasarar kashe wutar kafin ta kazance.
Mutum na farko mai suna Mista Jumo ya mutu ne a cikin dakin da yake zaune a yayin da mace ta biyu ta kwanta dama a lokacin da Likitocin Asibitin koyarwa na Jami’ar Bowen da ke Ogbomoso suka yi kokarin ceton ranta daga irin kunar wuta a sassan jikinta.
Yanzu haka manyan mutane da ’yan siyasa suna can suna ziyartar gidan domin gane wa idanunsu irin barnar da gobarar ta yi, tare da jajanta wa iyalan marigayan.
Har zuwa lokacin rubuta wannan labari babu wani labari da ya fito a hukumance dangane aukuwar wannan lamari.
Aminiya ta yi Kokarin jin ta bakin ofishin jami’an kashe gobara na Ogbomoso ba tare nasara ba.