✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta cinye daki da shaguna 7 a Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano a yau Laraba ta ce, an samu tashin gobara a hanyar Weatherhead da ke Sabon Gari a birnin jihar,…

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano a yau Laraba ta ce, an samu tashin gobara a hanyar Weatherhead da ke Sabon Gari a birnin jihar, inda ta cinye daki daya da shaguna bakwai.

Kakakin hukumar, Alhaji Saidu Mohammed, ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai NAN hakan wani tattaunawa da ya yi a Kano.

Mohammed ya ce, gobarar ta fara ne da misalin karfe 2:19 na tsakar daren Laraba kuma har yanzu ba a tantance asarar da gobarar ta yi ba.