Ga dukkan alamu gobara ta sake barkewa a gidan babbar jam’iyyar adawa ta kasar nan wato PDP, wadda ta sake shiga rudu, makonni kadan da faduwarta a zaben Shugaban Kasa.
A ranar Talata da ta gabata ce, Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na Kasa (NWC), ya ayyana Ambasada Iliya Umar Damagum a matsayin Shugaban Riko na jam’iyar ta kasa.
- Abba Gida-Gida ya daina riga malam masallaci —Ganduje
- Kwamandan Hisbah ya yi bankwana da ma’aikatan hukumar
Kafin nadinsa, Alhaji Iliya Damagum shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Shiyyar Arewa.
Kakakin Jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba ne ya bayyana nada Damagun a ranar Talata a wani taron manema labarai a Abuja.
A sanarwar da PDP ta fitar, ta ce ya zame mata dole ta yi biyayya ga umarnin wata kotu da ta bukaci Shugaban Jam’iyyar na Kasa Dokta Ayu Iyorchia ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan kararsa da aka kai gabanta.
Wata Babbar Kotu a Jihar Benuwai ce ta dakatar da Dokta Iyorchia Ayu daga shugabancin Jam’iyyar PDP ta Kasa.
Alkalin Kotun, Mai Shari’a W.I Kpochi ne ya bayar da umarnin a ranar Litinin bayan sauraron kunshin karar da aka shigar Mai lamba MHC/85/2023.
Tun a ranar Juma’ar da gabata Jam’iyyar PDP ta ce ta dakatar da Shugabanta na Kasa, Iyorchia Ayu bisa zarginsa da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.
Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke Karamar Hukumar Gboko, a Jihar Benuwe ne suka dauki matakin.
Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kada kuri’ar rashin kwarin gwiwa kan ayyukansa.
A lokacin da ya karanta matsayar da shugabannin suka cim ma, Sakataren Jam’iyyar a Gundumar Igyorob, Mista Banger Dooyum ya ce zagonkasa da Ayu da na kusa da shi suka yi wa PDP ne ya janyo mata shan kaye a gundumar da kuma jihar baki daya a zaben Gwamnan da aka yi a jihar.
Sun kuma zargi Ayu da rashin biyan kudaden da ake karba na shekara-shekara daga ’ya’yan jam’iyyar, kamar yadda dokokinta suka tanada.
Sai dai a martanin kungiyar yakin zaben Atiku mai suna Atiku Grassroots Mobement ta bayyana dakatar da Ayu a matsayin shiririta, inda a cewar kungiyar, an tursasa jagororin jam’iyyar na mazabar Agyorob ne su dauki wannan mataki.
Shugaban Kungiyar, Terzungwe Atser ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, inda a ciki ya ce ba zai taba yiwuwa jagororin jam’iyyar su dauki wannan mataki ba a yanzu ba tare da an tursasa su yin hakan ba.
Yanzu aka fara rigimar —Wike
A bangaren Gwamnan Jihar Ribas, Nyesome Wike ya ce yanzu aka fara rigimar siyasa a tsakaninsa da dakataccen shugaban na PDP, Dokta Ayu.
Ya ce hankali ba zai dauka ba a ce wanda ya kasa kawo mazabarsa a zabubbukan da suka gabata ya ci gaba da jagorantar PDP a matsayin Shugabanta na kasa.
Wike ya bayyana haka ne lokacin da yake kaddamar da makarantar Okoro-nu-Odo da ke Karamar Hukumar ObioAkpor da ya sabunta.
Ya ce, Allah ne kadai Ya san dalilin da Ayu ya kekeshe zuciyarsa ya ki sauka daga mukaminsa a lokacin da Gwamnoni 5 da ake kira G5 suka bukaci hakan bayan Atiku Abubakar ya zama dan takarar Shugaban Kasa a PDP.
Gwamna Wike ya ce da a ce lokacin da suka bukaci haka, Dokta Ayu ya amince ya sauka, da irin su da suka yi kokarin ganin an mayar da mulki Kudu sun yi amfani da wannan wajen samun sulhu, wanda a cewarsa watakila da hakan ya sa Jam’iyyar PDP ta samu nasara.
“Ku wadanda kuke cewa kun dakatar da Ayu, ba ku ma ga komai ba.
“Ayu, yanzu aka fara rigimar nan. Wadanda suke kusa da shi su fada masa cewa yanzu aka fara,” in ji Wike.
Duk da cewa ba yanzu aka fara yunkurin cire Ayu daga Shugaban PDP na Kasa ba, wannan karon lamarin ya yi karfi matuka domin a cikin shugabannin jam’iyyar da masu ruwa-da-tsaki an samu rabuwar kai kan cire shi.
Aminiya ta samu labarin cewa an fara yunkurin ganin bayansa ne kwanaki kadan bayan zaben Shugaban Kasa, inda Jam’iyyar PDP ta sha kaye a hannun Jam’iyyar APC, rashin nasarar da wasu suka alakanta da kin amincewa ya sauka daga mukaminsa.
Aminiya ta ruwaito yadda hayaki ya fara tashi a jam’iyyar bayan Atiku Abubakar ya doke Gwamna Wike na Ribas a zaben fid-da-gwan na takarar Shugaban Kasa.
Gwamna Wike da wasu gwamnoni hudu sun ware, inda suka kafa Kungiyar G5, wadda daga cikin bukatunta akwai batun cire Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar.
A cewarsu, ba zai yiwu ba dan takarar Shugaban Kasa da Shugaban Jam’iyya su fito daga yanki daya, wanda hakan ya sa suka bukaci Ayu ya sauka, a musanya shi da wani daga Kudu.
Hakan ya sa PDP ta shiga zaben Shugaban Kasa ba tare da gwamnonin biyar tare da ita ba, ciki har da Wikem, Gwamnan Jihar Ribas wadda take kan gaba wajen ba PDP kuri’u a zabubbukan baya.
Aminiya ta samu labarin cewa wannan yunkurin ya kara zafi ne kasancewar shugaban ya kasa hada kan jam’iyyar kafin zabe da kuma gazawarsa wajen kawo wa PDP jiharsa a zaben Shugaban Kasa da na gwamnoni, duk da cewa ba sa ga maciji da Gwamnan jiharsa ta Binuwai daya daga cikin gwamnonin G5.
Wasu abubuwan da suka kara ta’azzara rikicin shi ne batun dakatar da wasu jiga-jigan Jam’iyyar PDP da suka hada da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema kuma ta bukaci Kwamitin Ladabtarwa na Jam’iyyar da ya binciki Gwamna Ortom na Binuwai.
Jim kadan bayan dakatar da Shema ne ya fitar da sanarwa, inda a ciki ya bukaci ko dai a janye dakatarwa, ko ta zama takardar sallamarsa daga jam’iyyar, domin a cewarsa ba zai yiwu a dakatar da shi ba, inda kuma aka ce dole za a dakatar da shi, to zai bar jam’iyyar.
Daga cikin wadanda suke gaba-gaba wajen ganin an cire Ayu, akwai gwamnonin G5, wato Gwamna Nyesom Wike na Ribas da Samuel Ortom na Binuwei da Seyi Makinde na Oyo da Okezie Ikpeazu na Abiya da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.
Akwai kuma wasu jigajigan jam’iyyar, ciki har da tsofaffin gwamnoni da suka hada da Ibrahim Shema da Cif Bode George da Ayo Fayose da sauransu.
Haka a cikin jagororin jam’iyyar, Aminiya ta samu labarin cewa an samu rarrabuwar kai a tsakaninsu, inda wasu suka amince a cire shi, wasu kuma suke tare da shi.
Akwai bayanan da suke cewa mai yiwuwa Dokta Ayu ya kalubalanci dakatar da shi da Kwamitin NWC ya yi a kotu, lamarin da ake jin zai kara rura wutar rikicin da ke cin jam’iyyar.