Wata gobara ta ƙone gidajen wucin gadi sama da 100 ma ’yan gudun hijira a sansanin ’yan gudun hijira na hukumar ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Monguno ta Jihar Borno.
Shaidu sun ce ba a samu asarar rai ba a gobarar da ta tashi da misalin karfe 10.40 na safe na ranar Alhamis da ta gabata, kuma cikin sauri ta bazu a unguwar, inda ta ƙona kayan abinci, da sauran kadarori masu ɗimbin yawa.
Majiyar da ke sansanin ta bayyana cewar an tura jami’an agaji zuwa wurin domin kula da jama’a da kuma hana sace-sacen kayayyakin jama’a da suka rage, yayin da jami’an kashe gobara tare da mazauna sansanin suka yi bakin ƙoƙarinsu wajen kashe wutar.
Tashin gobarar dai ba shi ne karo na farko ba a wannan sansanin, domin ko da a kwanakin baya ma an samu makamancin hakan, lamarin ya sa jama’a ke zargin akwai sakaci daga wasu mazauna wannan sansanin.
- Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima
- Zaɓen 2027: Babu ɗan takarar da zai yi nasara ba tare da goyon bayan Arewa ba — Hakeem
Don haka suka jadadda buƙatar a riƙa yin hattara don kauce wa ci gaba da faruwar irin haka nan gaba, kasancewar yanayin bazara mai dauke da iska ne ke ƙara ƙaratowa a wannan yanki, wanda hakan kan haifar da barazanar yawaitar tashin gobara a lokacin bazara.