Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya bayar da gudunmuwar naira miliyan 30 ga mutanen da suka tafka asarar dukiya a gobarar da ta lakume wani sashe na babbar kasuwar Sakkwato a ranar Talata.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan jihar Sakkwato, Muhammad Bello ya fitar a ranar Talata, 18 ga watan Janairun 2021.
- Rigimar Kwankwaso da Ganduje tana kawo wa Kano cikas — Mu’azu Magaji
- An gurfanar da wani Uba da kaninsa kan zargin yi wa diyarsa fyade a Ekiti
- ’Yan sanda sun kashe masu satar mutane 2 a Filato
Gwamna Bagudu shi babban mutum na farko da ya kai ziyarar ga takwaransa na Jihar Sakkwato, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, inda ya jajanta masa dangane da musibar da ta auku da sanyin safiyar ranar Talata.
Ya ce jajantawa ita ce manufar ziyarar da ya kai wa Gwamna Aminu Tambuwal, inda ya jaddada cewa duk wani abu da ya faru a jihar Sakkwato ya shafi tasa jihar.
A nasa jawaban, Gwamna Tambuwal bayan godiya mai tarin yawa ga takwaransa nasa, y ace wannan gudunmuwa da ya bayar shaida ce a kan kyakkyawar dangartakar da kuma ’yan uwantaka da ke tsakanin jihohin Sakkwato da Kebbi.
Ya ce an samu gagarumar nasara a yayin da babu rai ko daya da ya salwanta a gobarar wacce jami’an Hukumar Kwana-Kwana na Jiha da na Tarayya suka sha fama wajen kashe ta.
Da yake yaba wa jami’an tsaron jihar kan irin goyon bayan da suka bayar wajen shawo kan lamarin, Gwamna Tambuwal ya roki Allah Ya yi wa Gwamna Bagudu da kuma jama’ar Jiharsa kyakkyawar sakayya musamman a wannan lokaci da ya jagoranci tawaga ta musamman da kawo jihar ziyara domin nuna damuwa kan halin da ta tsinci kanta.