✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gizagawan Najeriya sun tallafa wa marayu a Funtuwa

A makon da ya gabata ne Kwamitin tallafa wa marayu na kungiyar Gizago ta Najeriya, a karkashin jagoranci shugaban kungiyar na kasa Muhammd Kabir Adam…

A makon da ya gabata ne Kwamitin tallafa wa marayu na kungiyar Gizago ta Najeriya, a karkashin jagoranci shugaban kungiyar na kasa Muhammd Kabir Adam Gombe. Ya kai tallafi ga iyalan daya daga cikin membobin kungiyar, Alhaji Usman Gombo Funtuwa, wanda ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 12.

Kwamitin wanda tsohon Sakataren kungiya na kasa, Malam Kabir Umar Sakaina yaa jagoranta ya hada da tsohon Kakakin kungiya na kasa, Malam Habu Tsoho. da wasu mambobi; sun kai tallafi na kayan abinci da aka kiyasta kudinsa zuwa Naira dubu 30. Kayan sun hada da buhun masara daya, buhun shinkafa daya, katan din taliya da katan din macaroni daya. 

Yayin da suka mika tallafin ga mahaifin marigayin, iyalan marigayi sun yi farin ciki har da zubar da hawaye. Sun yi godiya tare da addu’ar albarka ga Gizagawa. An kuma yi wa mamacin addu’ar Allah Ya rahamshe shi, ya raya zuri’ar da ya bari.

 

Albishirinku Gizagawa:

 

Ina GIZAGAWAN NAJERIYA na dauri? Jirgin yaukaka zumunci ya kankama, duk Bagizagen da yake cikin wannan jirgi ya kara daura bel, wanda bai shigo ba kuma ya yi harama ya bazamo, domin kuwa gaf yake da fara tashi. Wanda duk ke bukatar shiga wannan kungiya ta sada zumunci da taimakon juna, sai ya tuntuba wadannan mutane a jihar da yake zaune:

Kano: Kabir Halliru Gogel (08039336748).

Jigawa: Sulaiman Ubali (07068178074).

Kaduna: Khalil Kabir Mantissa (08066039123).

Katsina: Bello Buhari Kaita (08169957978).

Zanfara: Murtala Korama Gora (08109984003).

Sakkwato: Yusuf dahiru (07035920066).

Kebbi: Umar Abaji Zamau (08037494622).

Adamawa: Mohammed Jungudo (07034924275)

Gombe: Muhammed Korau (08035406099).

Yobe: Ado Ibrahim Kwaya (08036257580).

Bauchi: Abdullahi Ilailah (08035748727).

Filato: Kabir SKB (08039335276).

Nasarawa: Shawilu Mohammed (08067809783).

Neja: Mohammed Auwal Ibarahim (08036281760).

Kogi: Ahmed Sulaiman Sani (07068626875).

Ondo: Ibrahim Yusuf (08034259434).

Oyo: Masiru Inuwa (08035231519)

Ogun: Salisu Shehu Shanono (08031111177).

Legas: Sirajo Yahuza (08081268044).

Ribas: Sa’idu Abubakar Badarwa (08036517450).