✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gizagawan Jihar Filato sun kai tallafi ga majinyata

kungiyar Gizagawan Jihar Filato ta yi abin kirki, domin kuwa a kwanakin baya ne suka kai tallafin kayan masarufi ga majinyata. Wakilinmu na Jos, Hussaini…

kungiyar Gizagawan Jihar Filato ta yi abin kirki, domin kuwa a kwanakin baya ne suka kai tallafin kayan masarufi ga majinyata. Wakilinmu na Jos, Hussaini Isah na daya daga cikin ’yan rakiya kuma ga rahoton da ya kalato mana, kamar haka:
kungiyar Gizagawa reshen Jihar Filato ta tallafa wa majinyata da suke kwance a asibitin La-Tahzan da ke Nasarawa filin kwallo, a garin Jos Babban Birnin Jihar Filato, da kayayyakin abinci.
Da yake jawabi a lokacin da ’ya’yan kungiyar suke mika kayayyakin tallafin, shugaban kungiyar na Jihar Filato Barista Rabi’u Yusuf, ya bayyana cewa manufofin wannan kungiya su ne taimaka wa gajiyayyu da marayu da marasa lafiya da suke kwance a asibiti da fursunoni da suke tsare a gidajen yari.
Ya ce don haka suka zo wannan asibiti domin su tallafa wa majinyatan da suke kwance a wannan asibiti. Ya ce sun zo da kayayyaki kamar taliya da madara da suga da dai sauran kayayyakin abinci.
Kamar yadda shugaban ya ce, dukkan irin wadannan ayyuka da ’yan kungiyar suke gudanarwa na tallafa wa al’umma, suna yi ne da kudaden da suke tarawa a junansu. Ya bai wa wannan asibiti tabbacin cewa za su ci gaba da kawo wa marasa lafiyar da suke kwance a wannan asibiti da sauran asibitocin da suke garin Jos tallafi.
Shi ma a nasa jawabin a lokacin da yake karbar tallafin, Daraktan asibitin na La-Tahzan, ya mika godiyarsu ga kungiyar kan wannan tallafi da suka kawo wa marasa lafiyar da suke kwance a wannan asibiti. Ya ce: “A gaskiya wannan abu da kuka yi wata karantarwa ce ga al’umma kuma wannan abu shi ne al’umma suke bukata a wannan lokaci da muke ciki, da jama’a suke neman wanda zai tallafa masu.”
Ya kara da cewa: “Wannan kokari da kuka yi, na tallafa wa masara lafiya, ya yi daidai da irin kokarin da muke yi a wannan asibiti.” Don haka ya yi addu’ar fatan alheri ga kungiyar.