Rahotanni sun bayyana cewa giwaye sun addabi manoma a yankin Gamboru Ngala na Jihar Borno da ke da iyaka da Kasar Kamaru.
Manoman sun yi kira ga hukumomi da su kai musu dauki saboda barna da giwaye suke yi wa gonakinsu a yankin.
- Akwai kararrakin zaben fidda gwani 600 a gaban kotu —INEC
- Zaben 2023: Za a raba wa ’yan sanda sabbin kayan aiki
Bayanai sun yi nuni da cewa giwayen sukan far wa gonakin mazauna yankin ne da tsakar dare su cinye musu amfanin gonakinsu.
“Gaskiya ba zan iya ce maka ga yawan giwayen nan ba. Yanzu gaba daya garin da daddare za mu fita mu kona tayu, muna kade-kade don mu kore su,” a cewar Alhaji Katomi, daya daga cikin mazauna yankin.
Muryar Amurka ta ruwaito cewa, ire-iren kayan amfanin gona da suke lalatawa sun hada da dawa, wake da sauran shuke-shuke a cewar mazauna yankin.
“Rokonmu shi ne gwamnati ko hukumomi masu zaman kansu, su tallafa mana,” in ji Alhaji Abba Greman Ngala.
Hadimi na musamman ga Gwamnan Jihar Borno, Abdulrahman Abdulkarim, wanda ya fito daga yankin na Gamboru Ngala, ya ce sun samu labarin wannan lamari kuma suna kokarin duba yadda za su magance wannan matsala, domin wannan ba shi ne karon farko da hakan ke faruwa ba.