✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girman kai rawanin tsiya

Barka da warhaka Manyan Gobe Ina fata kuna cikin koshin lafiya, Allah Ya sa haka, amin.  A yau na kawo muku labarin ‘Girman kai rawanin…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Ina fata kuna cikin koshin lafiya, Allah Ya sa haka, amin.  
A yau na kawo muku labarin ‘Girman kai rawanin tsiya’. Labarin ya kunshi yadda jiji-da-kai mutum ga halaka.
A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Girman kai rawanin tsiya

A wani kauye an yi wata kyakkyawar yarinya mai suna Sa’adiyya. Tana da matukar kyawu, yadda duk wanda ya kale ta sai ya kara.
Saboda irin halittar da Allah Ya yi mata sai kowa ke son ya yi alaka da ita. Ganin hakan, sai ya sa ta fara jiji-da-kai inda ta rika ganin kanta kamar sarauniya. Idan an gaishe ta ma da kyar take amsawa. Wata sa’in ma ba ta amsa gaisuwar ganin cewa wanda ya gaishe ta bai kai ya yi mata magana ba.
Rannan sai ta isa aure, mazaje da dama suka zo nemanta amma da ta ga mutum talaka ne sai ta ki aurensa.
A kullum sai mahaifiyarta ta yi mata fada da cewa kyawu tsufa yake, amma Sa’adiya ta ki jin nasihar da ake mata.
Rannan sai wani kyakkyawan saurayi mai kudi ya zo neman aurenta. Ashe mutumin dodo ne. bayan an yi auren ne ya dinga gallaza mata azaba. Ba abinci sai duka.
Ana hakan sai wata tsohuwa ta zo ta taimaka mata ta koma gida. Dagan an bat a kara yi wa wani wulakanci ba. Ta daina jiji-da-kai.
Da fatan Manyan Gobe za su  dauki darasi a wannan labarin da kuma zama masu saukin kai.