Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na girke-girke. Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka gasashen kifi. Nasan daga jin an ce gasashen kifi da yawa daga cikin mata za su dauka cewa za a gasa kifi ne kawai. To ba hakan take ba. Wannan irin gashin dai sai a gidan wane da wane ake yinsa, ko kuma a manyan wajen sayar da abinci. Idan an koyi wannan girkin, ba sai an wahala wajen kashe kudi da yawa domin samun irin wannan girkin ba. Girkin gida ya fi armashi da auki.
A sha karatu lafiya.
Abubuwan da za a bukata
• Kifin karfasa/tarwada
• Attarugu
• Magi
• Takaddar ‘foil’
• Tafarnuwa
• Albasa
• Man gyada
• Kori
Hadi
A samu kifin tarwada sannan a wanke da ruwan kanwa, ta yadda karnin zai fita tsaf. Sannan a wanke da ruwa. A kunna mukubur (rishon garwashi) ya yi zafi sannan sai a dauki karfen gashi akai. A yayyyanka albasa da jajjaga attarugu sannan a zuba a daura kifi akan takardar ‘foil’ a daka magi sosai yadda zai ratsa cikin kifin a zuba. Sannan a zuba jajjagen attarugun tare da yankakkiyar albasa a ciki. a barbada garin tafarnuwa kadan a ciki da dan kori. A shafa man gyada kadan a takardar ‘foil’ din kafin a zuba sauran kayan hadin a ciki. sai a nada takardar kamar sau biyu zuwa uku. Sannan a dora akan wutar garwashi. A bari ya gasu na tsawon mintuna 15 sannan a sake juya dayan gefen shi ma ya gasu na tsawon mintuna 15. A kalla dai an samu mintuna 30 ke nan. Sannan a bude a ci dadi. Za a iya yi wa maigida irin wannan girkin ko don more rayuwa.
Girkin gasashen kifi
Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na girke-girke. Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na…