Kawo yanzu, akalla mutum 1,305 ne suka mutu a girgizar ƙasar da ta faru a Morocco.
Ma’aikatar cikin gidan kasar ta sanar ranar Asabar cewa yawan wadanda suka jikkata sun karu zuwa 1,832, ciki har da mutum 1,220 da ke cikin mawuyacin hali a sakamakon wannan iftila’i.
Kakkarfar girgizar kasar ta auku ne a cikin daren Juma’a, inda ta lalata gine-gine a kauyukan da ke yankin tsaunukan Atlas, har zuwa birnin Marrakech mai dimbim tarihi.
Girgizar kasar mai karfin maki 6 da digo 8, ita ce mafi karfi da aka taba fuskanta a yankin, kuma mahukunta sun ce akwai yiwuwar adadin mamata ya karu.
Garuruwa da dama ne wannan girgizar ƙasar ta shafa, inda tun da farko mazauna birnin Marrakesh suka ce an samu katsewar lantarki.
Wannan kuma ya shafi intanet ɗin garin, wanda yanzu haka aka ambato babu sabis.
“Mun ji wata mahaukaciyar girgiza. Daga nan na fahimci cewa girgizar kasa ce. Mutane sun fada cikin firgici da yamutsi. Yara suna ta kuka yayin da iyaye suka dimauce,” kamar yadda Abdelhak El Amrani, wani mazaunin Marrakesh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ta wayar tarho.
Tuni shugabannin kasashen duniya suka fara aikewa da sakonnin nuna goyon baya ga kasar Morocco, biyo bayan wannan al’amari da ya same su, inda a wata sanarwa shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana alhininsa a game da asarar rayuka da kadarori da girgizar kasar ta haddasa.
Shi ma shugaban China, Xi Jinping ya aike da sakon ta’azziya ga al’ummar Morocco, yana mai bayyana fatan cewa kasar za ta murmure daga wannan iftila’i da ya same ta.
Rahotanni sun ce wurin da wannan girgizar kasar ta fi kamari yana da wahalar kutsawa ga masu gudanar da aikin ceto, abin da ke sanya fargabar karuwar adadin wadanda al’amarin ya rutsa da su.
An ji karar girgizar kasar a Algeria da ke makwabtaka da Morocco, ko da yake Jami’an Tsaron Algeria sun ce ba ta yi wata barna ba.
A 2004, akalla mutum 628 ne suka mutu yayin da 926 suka jikkata sakamakon girgizar kasar da ta auku a Al Hoceima da ke arewacin Morocco.