Wata girgizar kasa mai karfin 6.3 a ma’aunin Richter ta afkawa kasar Croatia tare da jikkata mutane da dama da kuma rusa gidaje masu yawa a garin Petrinja dake Kudu maso Gabas da babban birnin kasar.
An yi girgizar kasar ne a ranar Talata a kusan duk fadin kasar da ma wasu makwabtan ta kamar su Sabiya da Bosniya da Herzegovina da ma yankin Graz na Kudancin Autria.
- A shirya wa annobar dake tafe bayan COVID-19 – Majalisar Dinkin Duniya
- Mace-macen da suka fi girgiza Najeriya a 2020
Gine-gine da dama ne suka rushe a birnin na Petrinja, mai nisan kilomita 60 daga birnin Zagreb.
An hangi masu aikin ceto na kokarin zakulo wani uba da dan sa da kasa ta danne a cikin motarsu daga cikin baraguzai.
Cibiyar Binciken Yanayin Kasa ta Nahiyar Turai ta ce guguwar kasar ta yi tafiyar kusan kilomita 46 a yankin Kudu maso Gabashin Zagreb, yankin da ko a ranar Litinin sai da wata girgizar mai nauyin 5.2 ta afka wa.
Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross a kasar ta ce girgizar ta yi matukar barna a yankunan da ta shafa.
Kafafen watsa labaran kasar sun rawaito cewa mutane da dama sun ji raunuka, ko da yake ya zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba, yayin da hanyoyin sadarwa suka kakkatse.
A birnin Zagreb, mutane sun rika guduwa kan tituna domin tsira da rayukan su, yayin da wasu da yawa kuma suka rika barin birnin, duk kuwa da dokar hana tafiye-tafiye da aka saka saboda annobar COVID-19.
Tuni dai aka rufe Tashar Nukiliyar Krsko ta Sloveniya a matsayin matakin ko-ta-kwana, inji kakakin cibiyar, Ida Novak Jerele a hirar sa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ranar Talata.