Girgirzar kasar Morocco ta ranar Asabar ta jefa al’ummar duniya cikin damuwa, sannan ta tuna wa ’yan kasar irin tashin hankali da suka shiga a lokua daban-daban a baya saboda irin wannan iftila’i.
Duk da cewa hukumar binciken yanayin kasa ta Amurka ta ce akwai yiwuwar samu girgizar kasa mai karfin a Morocco, sai dai ba kasafai ba; amma wadanda aka samu a kasar a baya sun jawo asarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa.
Ga jerin wasu mafiya munin girgizar kasa da aka samu a Morocco a tarihi:
1- Lashbona – 1755
Girgizar kasa mafi muni a kasar ta auke ne a yankin Lashbonah da ke Arewacin kasar Morocco a 1755, shekaru 268 da suka gabata.
An yi kiyasin cewa karfinta ya kai maki 9 kuma ta kashe mutane kimanin 60,000 zuwa 100,000, ta lalata kusan daukacin yankin na Lashbonah da kuma Al-Dar Al-Baida’, cikin dan takaitaccen lokaci.
2- Agadir – 1960
Makamanciyar girgizar kasar mafi barna a baya-bayan nan a Morocco ita ce ta shekarar 1960 a yankin Agadir mai karfin maki 5.8.
Girgizar kasar ta kashe mutum 15,000 (kashi daya bisa ukun al’ummar yankin) a cikin dare, wasu mutum 12,000 suka jikkata, kimanin 35,000 kuma suka rasa muhallansu, sannan ta lalata kimanin kashi 70 abubuwan more rayuwa a yankin da ke gabar Tekun Atlantic.
Uwa uba, tsananin zafin rana a lokacin ya sa gawarwaki saurin rubewa a karkashin baraguzan gini, wanda hakan ya haddasa barkewar cuta.
3- Al Hoceima – 2004
A daren 24 ga watan Disambar 2004, girgizar kasa mai karfin maki 6.3 a birnin Al Hoceima da ke gabar kogin Arewacin kasar ta kashe mutum akalla 628 a lokacin da suke tsaka da barci, galibinsu mazauna yankunan karkara; wasu 926 suka samu rauni, akalla 15,000 suka rasa matsugunansu.
Karfinta ya kai ga lalata gine-gine a yankunan da ke makwabtaka da Al Hoceima.
Washegari, mutanen da suka rasa muhallansu suka gudanar da zanga-zanga kan rashin tallafi daga gwamnati. Mutane da dama sun samu rauni a yayin dauki-ba-dadin da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da sojoji.
Bugu da kari! An sha samun girgizar kasa a yankin na Al Hoceima, mafiya shahara daga ciki su ne ne shekarun 1910 da 1927 da kuma na 1994 mai karfin maki 5.4 wanda ya rusa dubban gine-gine, musamman a kauyukan yankin.
1719 – Yankunan gabar kogi
A shekarar 1719 kuma, yankunan da ke gabar kogi a kasar suka samu girgizar kasa da ta yi barna mai munin gaske har a birnin Marrakesh.
1722
A ranar 27 ga watan Disambar 1722 kuma an samu wata girgizar kasa mai karfi da ta yi gagarumar barna a wasu daga cikin yankuna da ke gabar teku.
Fiye da sau daya
Baya ga haka, a kasar ta Morocco an samu akwai yankuna da dama da aka samu girgizar kasa, ba sau daya ba, inda a wasu lokuta iftila’in kan rushe unguwanni gaba daya.
Daga cikinsu akwai wadannan:
Aghadir: Shekarar 1731 da kuma 1761.
Fas: 1522 dakuma 1624.
Maliliyyah: 1660 da 1578.
Marrakesh: 1719 da kuma 1755.
Dama-dama
Akwai kuma wasu girgizar kasa masu karfi da aka samu a kasar, amma Allah Ya takaita yawan samu mace-mace da aka samu
1969: A watan Maris na shekarar 1969 kuma aka samu girgizar kasa mai karfin maki 7.8, a yankin Zirin Gibralta, inda ta kashe mutane 11 a Morocco da Portugal, tare da yin matsakaicin lahani ga gine-gine.
2016: A watan Janairun 2016, girgizar kasa mai karfin maki 6.3 da aka samu a Tekun Alboria a yankin Al Hoceima da kuma kasar Spain ta yi ajalin mutum daya tare da jikkata wasu 26 a yankin Meilla da ke kan iyakarta da kasar Spain.