✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ginin matatar man Dangote

Shirin da rukunin Kamfanonin dangote ke yi na gina matatar man fetur da za ta rika tace gangar mai dubu 400 a kowace rana, ta…

Shirin da rukunin Kamfanonin dangote ke yi na gina matatar man fetur da za ta rika tace gangar mai dubu 400 a kowace rana, ta kuma samar da takin zamani a Najeriya, al’amari ne da aka dade an hankoron samunsa, don bunkasa tattalin arzikin kasar da ke salwantar da duban biliyoyin Naira wajen shigo da albarkatun man fetur a sawon shekaru. Ga kasa irin Najeriya, wadda ke cikin jerin kasashen da suka fi fiutar da gurbataccen mai da iskar gas  zuwa kasashen duniya, dimbin alfanun da jarin Kamfanin dangote zai samar ba karami ba ne. Bisa la’akari da girman wannan matata, ana sa rana Najeriya ta rage  dogaro da kimanin rabin tatatcen man da ake shigowa da shi, sannan a toshe kafar sata a “gungun masu cuwa-cuwar tallafin mai,” wadanda suka shafe tsawon shekaru suna kashe mu raba akwangilolin shigo da mai da gwamnati ke bayarwa. Sannan jami’an gwamnati sun doge kan cewa lallai kasar nan ba za ta iya wadata kasar isasshen man da take bukata ba, domin fakewa da wannan mumunar dabarar su fitar da gurbataccen man fetur a kan farashi mai rahusa, sannan su shigo da tattatu da sarrafaffun albarkatun man kan kudi tsagwagwa.
Ana sa ran kammaluwar fara aikin matatar nan da shekarar shekarar 2016, al’amarin da ake san kudin da kimarsu ya kai Dala biliyan tara. Rukunin kamfanonin dangote, a karkashin jagorancin Alhaji Aliko dangote, hamshakin mai arzikin Afirka, za ta zuba jarin Dala iliyan hudu, sannan a rattaba hannu kan yarjejeniyar rancen kudi da cibiyoyin hada-hadar sarrafa kudi 12 na cikin da na waje, wadanda za su samar da Dala biliyan uku da miliyan 300, inda ragowar kudin zai fito daga sauran masu saka jari, na cikin gida da na ’yan kasashen waje. Za a samar da aikin yi ga injiniyoyi dubu akwas da kwararrun masu ayyukan hannu, sannan wasu mutu dubu biyar za su shigo a ria damawa da su.
Wasu masu saka jarin sun fara nokewa wajen zuba dukiyarsu a harkokin man fetur da sauran sinadarai, duk da cewa gwamnati ta ba su daukacin tallafin da ya dace, wadanda suka hada da tashoshin wutar lantarki da sauran kwangiloli gwababa kan tsarin yarjejeniya mai saukin bi. A shekarar 2002, an bayar da lasisin gina matatu ga kamfanoni masu zaman kansu har 12, amma daga bisani, bayan shekara biyar sai aka soke, saboda sun nuna gazawa wajen amfani da damar da suka samu. Jami’an gwamnati da kwararrun masana sun yi ta kokarin yin bayani game da rashin sha’awar da kamfanoni masu zaman kansu ke nunawa, saboda ba su kaunar a daina bin tsarin biyan kudin tallafin man fetur da rashin tsaro don kada a kawo musu cikas. Jami’ai da masu bayar da shawara kan tattalin arziki, sun tabbatar da cewa sai Najeriya ta jajirce wajen yin duk abin da ya dace game da sarrafa albarkatun man fetur, sannan a samu masu saka jari a cikin gida da kasashen waje, wadanda za su gina matatar mai. Tabbas Hukumar Gudanarwar Rukunin Kamfanonin dangote da sauran masu saka jari sun auna kimar asarar da ke tattare da shirin kafin su shiga cikin harkar. Wannan yunkuri ne da zai samar da dimbin alfanu a harkokin kasuwanci. Wannan kishin kasa ne, kuma nuna kwarin gwiwa ne ga bunkasar tattalin arzikin Najeriya.
Takaddamar da ka sha yi a baya, ita ce kwatanta farashin aiwatar da aikin a halin yanzu, wanda gwaggwaba ne ga duk mai bukata ko masana’antar da ke shirin fara tatar mai a cikin gida, fiye da asarar da ke tattare da shigo da tattatun albarkatun man fetur, bayan an biya kudin rariya taken mai da kudijn dako zuwa matatun kasashen waje, sannan a sake biyan kudin safarar man ta jirgin zuwa zuwa Najeriya. Ko ta wace mahanga a dubi wannan al’amari, za a fahimci cewa kafa matata kusa da inda ake samun abubuwa da za a sarrafa da kusanci da kasuwanci su suka fi alfanu. Kai hatta ga abin da ya shafi tsaron kasa, kokarin Najeriya wajen biyan bukatun al’ummar kasa ya zama dole a dcauke shi da muhimmanci.
Harkar tsaro na da matukar muhimmanci, kuma wajibi ne gwamnati ta yi duk abin da za ta iya yi, don shawo kan wannan matsala, saboda gudun kada a rika kai hare-hare kan amtatun mai, kuma a kawo cikas wajen samar da gurbataccen man. Matukar babu isasshen gurbataccen, to ai babu abin da za a tace ke nan.
Duk da cewa rukunin Kamfanonin dangote sun canci yabo, ya kamata wannan al’amari ya zama karin kwarin gwiwa da karsashi ga masu saka jari a cikin gida ko min kankantarsa. Bunkasar wannan kasar da samar da isasshen makamashi da daidaituwar al’amuran siyasa, na bukatar cikakken dogaro da kai, ta sarrafa albarkatun man fetur a amtatun cikin gida, inda za a rika samar da fetur da kananzir da takin zamani da sauran sinadarai, wannan bai takaita ga nan ba, har ma da samun karfin fitar da hajja zuwa kasuwanin duniya, don samun kudaden musaya.