✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ginin bene ya rufta kan mutum 10 a Kano

Wani ginin bene da ya rufta a unguwar Gwammaja ’Yan Kosai da ke karamar hukumar Dala a Jihar Kano ya hallaka mutum biyu yayin da…

Wani ginin bene da ya rufta a unguwar Gwammaja ’Yan Kosai da ke karamar hukumar Dala a Jihar Kano ya hallaka mutum biyu yayin da mutum takwas suka jikkata.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ta jihar, Sa’ idu Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin yana cewa jami’an hukumar sun ceto mutum takwas, wadanda ginin benen ya danne, da ransu; sun kuma gano gawarwakin mutum biyu.

“Da misalin karfe 1:37 na ranar Talata muka samu labarin rushewar benen kuma nan take jami’anmu suka isa wurin domin kai dauki.

“Ginin benen mai hawa daya ya danne mutum 10 da ke cikin gidan inda muka ceto takwas daga cikin su yayin da likitoci suka tabbatar da Allah Ya yiwa mutum biyu cikawa”, inji shi.

Ya kara da cewa an garzaya da wadanda suka jikkata asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano domin a ba su kulawa..

Sa’idu Muhammad ya yi kira ga jama’a a jihar da su dinga lura da yanayin muhallin da suke zaune domin kare aukuwar irin haka.

%d bloggers like this: