An tabbatar da mutuwar wani lebura yayin da wani gini ya rufta kansa a yankin Aromire da ke tsakiyar Ikeja a Jihar Legas.
Ginin mai hawa daya wanda ake aikin gyaransa ya rushe sannan ya danne wasu leburori da ke aikinsa.
- An kama Sarakuna biyu kan harin tashar jirgin kasan Edo
- Emefiele ya sake kai wa Buhari ziyara a sirrance
An ruwaito cewar ginin ya kasance yana dauke da wata shahararriyar kasuwar sayar da mota a yankin.
A cewar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), “Ma’aikatan da ba su da kwarewa ne ke gudanar da aikin, wanda ya haifar da rugujewar wani bangare na ginin.”
Sakataren LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu ya bayyana cewa wani ma’aikaci daya ne ya rasa ransa yayin da wasu suka ji rauni
Ya ce, “Binciken da aka gudanar ya nuna cewa ginin ba shi da wata alamar rushewa.”
A halin da ake ciki an rufe ginin yayin da hukumar kula da gine-gine ta jihar (LASBCA) da ‘yan sanda za su ci gaba da gudanar da bincike.