Wani dogon gini mai hawa 10 a birnin Abadan na Iran ya rushe.
BBC ya ruwaito cewa lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum akalla biyar tare da raunata wasu fiye da 20.
- Labaran Aminiya: Amurka Za Ta Tallafa Wa Kasashen Afirka 10 Da $215m
- An yi zanga-zanga a Spain kan dawowar tsohon Sarki Juan Carlos
Ganau sun shaida wa kungiyar agajin gaggawa ta Iran cewa akwai mutane akalla 80 da suka makale a baraguzan ginin.
Wasu hotuna da aka dauka a Abadan sun nuna mutanen da ke zaune a ginin sun hallara tare da nuna fargaba da fatan zakulo wadanda ba a kai ga ganowa ba.
Kwanaki biyu da suka gabata ne mutum biyu suka mutu yayin da wasu mutum uku suka jikkata a sakamakon rushewar wani gini a yankin Alayaki na Jihar Legas.
Kazalika, kimanin mutum 10 ne suka rasa rayukansu a ranar Lahadi, 1 ga watan Mayu, a sakamakon rushewar wani gini mai hawa uku a Unguwar Ebute Metta da ke birnin Ikkon na Legas.
Hukumomi a Najeriyar na danganta yawaitar rushewar gine-gine da rashin bin tsarin gini da ma rashin ingancin aiki.