✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gine-Ginen Gidan Sarautar Kano: Jiya da Yau (2)

Zamanin Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero dan Sarkin Kano Muhammadu Abbas (1926-1953) wanda ya yi Ciroman Kano kafin zamansa Sarki, kuma shi ne Sarki na…

Zamanin Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero dan Sarkin Kano Muhammadu Abbas (1926-1953) wanda ya yi Ciroman Kano kafin zamansa Sarki, kuma shi ne Sarki na farko da ya fara zuwa aikin Hajji, a zamanin da yake kan gadon mulkin sarautar Kano. Ya gudanar da mulki ne qarqashin Turawan mulkin mallaka, amma duk da haka Sarki Alhaji ya rushe babban masallaci, ya gina babban masallacin juma’a na Kano, wanda a lokacin ginin qasa ne, shi ne ya sake gina shi kamar yadda yake a yanzu. Har ila yau, ya sake gina wasu soraye da bukkoki na kwanciyar bayi kuma ya sake wasu rufin dakuna da suka yaye lokacin damina, wasu kuma sun ce lokacinsa ya maida hankali sosai wajen yin ayyukan jin dadin talakawansa da bayinsa. Tun daga muhalli zuwa sutura da abinci a zamaninsa bayin Sarki sun samu kulawa.

Sarkin Kano Sa, Khalifa Muhammadu Sanusi I, babban dan Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero (1953-1963). Ya yi Ciroman Kano kafin zamansa Sarkin Kano. Ya fara gudanar da mulki qarqashin Turawan mulkin mallaka, a zamaninsa ne kuma Najeriya ta samu ’yancin kai a 1960 daga hannun Turawan mulki. A zamaninsa, shi sarki ne mai kwarjini da muhibba da kuma fada a ji. Tarihi ya nuna an yi wata gobara a wajen bukkokin bayi a lokacin da ake yin alewar madi. Dalilin wannan gobara sarki ya sanya duk aka rushe bukkokin gidan masarautar Kano, aka yi ginin qasa mai kyau, aka yi rufin azara. An yi gyaran katanga tare da gina soraye na alfarma; ciki kuwa har da soron Ingila wanda aka gina domin zuwan sarauniyar Ingila, wacce ta ziyarci masarautar Kano a 1956.
Ayyukan da Sarki Muhammadu Sanusi I ya yi a bangaren ilimin zamani ma, Abdulrahman Sarkin Kotso ya bayyana su a waqar ‘Mamman Zakin Daga na Abashe.’

“Zamanin dan Audu niqatau
Birnin Kano ko ana an qaru
Ga makarantu an yi fiyayyu
Ga siniya sakandare na nan
Furobishal sakandare na nan
Ga siniya firamare na nan
Ga makarantun mata na nan
Iliminmu yau ya kai ga kwaleji
Ga Bayero Kwaleji tana nan
Makaranta babba a Nauzan
Duk a qasashe babu irinta
Sai Kano garin Mamman na Abashe
Sa Sanusi sarkin yaqi, zakin daga na Abashe.”
Ayyukan da ya yi cikin gidan Sarautar Kano, Jankidi ma ya kawo su a waqarsa;
Salihu Jankidi
Arziki ya yi kai as Sarki, yau Sanusi ka mulkin Kano
“An yi ofis Kano hawa biyu,
Najeriya Arewa kwata,
Anyi ofis Kano hawa biyu,
Najeriya Arewa kwata,
Ba wanda adda ofis haka,
Fanka uku,
Hitila hudu.
Nan wurin zaman Sarkin Kano.
Babban malami dag gabas,
Dag ga nan yamma yaran Sarki,
Ga wuqa ga takobi rataye,
Ga harabar zaman ’yan kara,
Dag ga huskar Arewa mata,
Ga hwonho, kuma ga magewayi,
Ga katanga ta dutsi ya yi,
Duk ya gyara gidan Alhaji,
Lallai mulki ya kammala,
Muhammadu Allah shi maka tsari,
Muhammadu Allah shi maka tsari,
Arziki ya yi kai as Sarki, yau Sanusi ka mulkin Kano.”
Sarki Sanusi ya yi gine-gine da dama ciki har da babbar fadar waje ta Qofar kudu da kuma ginin benenta.
Sarkin Kano Muhammadu Inuwa dan Sarkin Kano Abbas (1963-1963). Duk da ana cewa wata shida kacal wannan Sarki ya yi a gadon sarautar Kano, an ce da hawansa ya sa a ka yi wasu zane na kwalliya a jikin garun masarautar Kano.
Sai kuma Sarkin Kano Alhaji (Dokta) Ado Bayero dan Sarkin Kano Abdullahi Bayero.
A zamaninsa ya qara inganta katanga wacce ta kewaye gidan sarautar Kano, a jikin garun kuma aka rangada zanen zayyana dada kyau. A zamaninsa ne ya ruguje wasu dakunan bayi ya zamanantar da ginin kuma aka yi lambu da shake-shuken kayan marmari da furannin alfarma a Shekar gabas domin a samu wajen hutawa. Ya gina wasu rukunin dakuna na zamani don kwanan Sarki. Sannan an gina wasu wurare a bangaren matan Sarki. A zamaninsa kuma aka gina asibiti a cikin gidan Sarki, sannan shi ne ya rushe gidan Shamaki Isiyaku ya gina ofishin Sarki da ofishin sakatarorin sarki, wanda har yanzu a cikinsa Sarki yake zama, sannan ya rushe gidan Galadiman Maitsidau da ake cewa Gidan Gawo, a wajen ya gina wata fada a tsakanin soron makaranta da soron hakimai.
A cikin gyare-gyaren da ya yi, ya gyara masallacin cikin gidan Sarki, ya gyara soron Giwa da soron Gabjeje da soron Zauna-lafiya da soron Ashafa da katangar Qofar Kudu. Ya kewaye filin Qofar Kudu da qarafa, ya qara gini a benen Qofar Kudu tare da yin rumfa, sannan daga gabas da Qofar Kudu nan ma ya yi wata rumfa domin yin taro. A zamaninsa ya yi wa gini da yawa goyo a cikin gidan sarki, cikin gine-ginen da aka yi wa goyon akwai Qofar Fatalwa da Kwaru da kuma Qofar Kudun.
Baya ga wadannan kuma an yi gyara-gyare da qawata sauran gidajen Sarki kamar gidan Nassarawa da Fanisau da Kuma dorayi, yawanci duk an rushe tsofaffin gine-gine na qasa, duk an mayar da na siminti a madadinsu.
In har iyaye da kakannin sarki sun yi wadannan ayyukan, shin me ye laifin Sarki Muhammadu Sanusi na II dan Ciroma Aminu dan Sarkin Kano Sa Muhammadu Sanusi I, don ya dora daga inda suka tsaya? Abin dubawa dai, duk cikin sarakunan Kano dama Sarki Sanusi I, shi ne ya rushe bukkoki ya yi ginin qasa da azara. Kuma duk cikin ’ya’yansa ba wanda ya hau kan gadon mulkin Kano sai yanzu da jikansa ya hau. Ba abin mamaki ba ne idan qwarya ta bi qwarya wajen maye gurbi.
Tunda cewa sai da tubali ake gini, tuni mai wannan qorafi mara dalili ya fuskanci cewa ya tafka kuskuren rashin duba tarihi kafin ya kai wannan qara maras tushe ko tudun dafawa, don haka yanzu ya janye yana mai cike da nadama.
Na samar da wannan rubutu ne saboda jama’a su samu gamsasshen bayani bisa tarihin gine-ginen dake gidan Sarautar Kano.
An kammala