Jam’iyyar APC ta jihar Kano ta zargi shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado da gilli kan kama tsohon kwamishinan ayyuka da ya yi.
Kakakin jam’iyyar APC a jihar Kano, Ahmed Aruwa ne ya bayyana haka bayan kotu ta tura Injiniya Wada Saleh zaman waƙafi zuwa 14 ga Yuli bisa tuhumar badaƙalar Naira biliyan guda ta gyaran hanyoyi.
Ahmed Aruwa ya ce dama jam’iyyar APC ta san za a yi haka saboda Barista Rimin Gado na da burin burge shugabannin da suka ɗora shi kan muƙamin da yake kai yanzu.
An kama kwamishinan Ganduje bisa badaƙalar Naira biliyan guda
Abba Kabir ya dakatar da ma’aikatan da Ganduje ya ɗauka
Ya ce “Ya faɗa da kansa zai gayyaci Gwaggo ma, ya faɗa da kansa zai gayyaci Abba, don haka an faro ne, kuma so ake a tabbatarwa da duniya wadannan abubuwa da ake so a yin an fara yin su tun yanzu.
“So a wajenmu ba wani abu bane, mu abinda ita jam’iyyar APC ta kalla a taka dai a hankali; Ita gwamnati gaskiya ce.
“Mai girma gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje gwamna ne zaɓaɓɓe kuma a wancan lokacin da yake bada umarni da jan biro, hukuncin da ya zaɓe shi ita ce ta ba shi wannan damar.
Sai dai kakakin na APC ya gargaɗi Barista Rimin Gado cewa jam’iyyar za ta iya bincikarsa duk lokacin da ta dawo mulkin Kano.