✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyata ba za ta shafi zaman aurena ba – Mansura Isah

Aminiya: Me ya ja hankalinki kika kafa wannan gidauniya taki? To da man na dade ina yin wannan aikin da ya shafi tallafa wa marayu…

Aminiya: Me ya ja hankalinki kika kafa wannan gidauniya taki?

To da man na dade ina yin wannan aikin da ya shafi tallafa wa marayu da kuma marasa karfi, sai dai nakan yi a boye ne ba tare da kowa ya sani ba, muna raba abinci da biyan kudin makaranta ga marayu, to da yake ka san idan mace ta yi aure yawanci abubuwa suna tsayawa, saboda idan ka duba kamar harkar fim din ne, mace mai aure ba ta da lokacin da za ta  zo  ta yi saboda yanayin tafiye-tafiya da ake yi.

Ta yaya aka yi kika koma ba da tallafi bayan kin samu lokaci ba kya yi saboda zaman aure?

Abin da ya faru shi ne, na tsaya na kalli yadda al’umma take a yanzu sai na ga ta ina zan bayar da tawa gudunmuwar, domin in samar musu da sauki a rayuwa, to sai na ga abin da ya kamata in yi, sai na dawo da tallafin nan da nake yi a baya, don haka sai na sanar da mijina, kuma na nemi shawara a gare shi, don haka sai muka tsara zan rika fita ina neman taimako a wajen jama’a, domin yanzu ba aiki nake yi ba, ballantana a ce kudade suna zuwa  mini kamar a lokacin baya ba.

Wannan ya sa na kafa wannan gidauniya mai suna ‘Today Life Foundation’ kuma na tallata ta a kafafen yada labarai, cewar duk wani mutum ko wata kungiya da take son tallafa wa marayu da marasa karfi, to a shirye muke mu hada karfi da su don ganin an tallafa musu, kuma mun buga takardu muka aika wa manyan masu kudi da kamfanoni domin su ba mu gudunmawa wajen taimaka wa masu bukata, kuma haka muke yi muna samun tallafi sosai daga wajen masu bukatar tallafa wa jama’a.

Kamar kuma yadda jama’a suke gani muna kai wa mabukata wannan tallafi, kamar abin da ya shafi gidajen marayu da na masu tabin hankali da asibitoci har ma anguwanni mukan shiga don raba irin wadanan kayayyaki da abinci, wanda mu muke dafawa mu raba. Wani lokacin kuma mu raba kudi saboda idan kana irin wannan aikin sai ka ga kowa da irin abin da yake bukata, don idan ka je asibiti za ka ga irin abin da ake bukata. Wani magani aka rubuta masa, ba shi da kudin siya, wani abinci yake bukata.

To wannan harka da alama dai ta shiga nan da fita can ce, ko wadanne irin matsaloli kike fuskanta?

A gaskiya muna fuskantar matsala sosai a cikin wannan aikin namu, matsala ta farko ita ce, yadda muke samun tsangwama da kuma zagi daga wajen mutane, don idan muka saka abin a social media sai ka ga wasu na zagi da fadar maganganu, wai ai wannan riya ce, to ni ina gani wannan ba daidai ba ne, Allah Shi ne ya san abin da yake cikin zuciyar bawanSa, amma sai ga shi ana yi mana hukunci. 

Sannan matsala ta biyu da muke fuskanta ita ce, wani lokacin kudi yana yanke mana, sai ka ga masu bukatar sun zo gare mu amma babu kudi a wajenmu, saboda mun ajiye lambar wayar mu ga duk wanda yake bukatar taimako ya kira mu.  

A kokarin ki na tallafa wa mabukata, kin shiga wurare da dama kamar gidan marayu da gidan masu tabin hankali da kuma asibitoci, ko wadanne irin nau’in mabukata kika gani da abin ya fi tayar miki da hankali?

To, zan iya ce abubuwa kamar guda uku zuwa hudu ne. Na farko, akwai lokacin da muka shirya kai tallafi asibotocin gwamnati guda 15 da suke cikin garin Kano. To da muka kai tallafin wajen asibitoci 13 sun fadi wasu abubuwa da suka girgiza ni, kuma da yake mu da yawa muka je su ma abin ya taba su. 

Domin da suka ga mu Musulmi ne muka zo kawo kayan tallafi abin ya ba su mamaki, kuma sun ji dadi sosai, saboda Musulminmu ba su cika yin wannan abin ba, sun ce sai ka ga Kiristoci sun zo sun raba biredi, su ce sun zo yi wa mutane addu’a, sai su bi daki-daki suna yin addu’a wani lokacin ma sukan zo ba tare da sun ba da komai ba, su ce sun zo ne su yi musu addu’a, sai ga shi mu da ake ganin ’yan fim ne, muka zo muka fara yin irin wannan abin. To wannan kalubale ne gare mu Musulmi. 

Na uku, akwai wani waje da muka je a can  Tudun Maliki, mun je wani gida na mutane da suke da wata cuta, kuma suke bukatar kulawa ta musamman, to abin da na gani ya girgiza  ni, kuma tsoron Allah da imani ya kara shiga zuciyata, don su wata irin cuta suke fama da ita,  don sai ka ga mutum dan shekara 30, amma yanayin jikinsa bai wuce na dan shekara tara ba, sannan ba sa iya yin magana, ba sa iya yin komai ko abinci za su ci sai dai su zubar a kasa su kwanta suna ci da baki. 

Don ba za su iya dauka da hannunsu su kai baki ba. Don haka sai dai su rika ci da baki suna lasar kasa. To duk lokacin da na tuna wannan abin na kalli kaina na kalli ‘ya’yana, sai na kara gode wa Allah. 

Don su wadannan mutanen saboda iyayensu ba sa iya kulawa da su, to sai a dauke su a kai su wannan gidan ya zama gwamnati ce take kula da su. Muna zuwa gidan marayu sai mu samu yarinya sabuwar haihuwa a ce da mu jiya aka tsince ta an jefar da ita a cikin bokiti, wani an yar da shi a cikin kwata, wata ma za ka ji an ce a bola aka jefar da ita. Kuma sai ka gan su kyawawa.

Wadanne irin nasarori kika samu a harkar wannan kungiyar taki?  

To, nasarorin da na samu a Today Life Foundation shi ne, taba rayuwar mutane ita ce babbar nasara, wato saka mutane farin ciki su yi murmushi na jin dadi. Mutum ya yi barci da farin cikin  tallafin da  muka yi masa , mu shiga inda yake mu faranta wa mutane rai.

A irin wanan yanayi naki na fafutukar samar da farin ciki ga mabukata akwai masu ganin cewar yanayin da Manzura Isah take fitowa ko dai ba ta da aure ne?

To ni ban san abin da ya sa mutane suke maganar ko ina da aure ko ba ni da aure ba, domin dai na farko wannan aikin ba zai hana ni zaman aure ba. Kuma wannan matsalar ita ce ma take kawo mutuwar aure. Sai ka ga mace tana harkokin kasuwancinta, tana samun kudi daga ta yi aure sai ta rufe kasuwanci ta koma zaman gidan miji. Daga karshe sai ka ga an tashi ke ba ki da shi, miji ba shi da shi, ga ’ya’ya an haifa, karshe sai ka ga yara sun galabaita. 

To ni ba haka nake ba, ina da ilimina, mijina yana da iliminsa, don haka ni zan nemi na kaina, shi ma mijina ya nema, mu hadu mu gina rayuwar ’ya’yanmu, don ba wanda ya san gawar fari. 

Idan ya riga ni mutuwa zan zo ina neman mijin da zan aura ya rike min ’ya’ya, ko kuma a lokacin zan fara neman sana’ar da za ta rike mu. Don haka ina da aurena kuma aikin da nake yi bai hana ni zaman aure ba.

Ita wannan kungiyar taki ko tana da alaka da siyasa?

To ita wannan kungiya Today Life Foundation ba ta siyasa ba ce, amma tana da alaka da ’yan siyasa sosai, domin abokan tafiyarmu ne ko yanzu aiki ya taso na siyasa kungiyar mu za ta yi shi, sai dai ba za ta shiga cikin siyasa ta narke ba. 

Kuma kamar yadda nake fada, kuma nake alfahari da shi ni Mansura Isah ni ce mace ’yar fim ta farko da ta fara yi wa dan takarar Shugaban kasa yakin neman zabe, ni ce jaruma ta farko da ta fara shiga siyasa, na yi wa shugaba Umaru Musa ’Yar’adua kamfen, na kira ’yan fim suka shiga. Don haka ko a yanzu wani dan siyasa ya nemi in yi masa yakin neman zabe, matukar ya dace da manufofina zan yi masa, kuma idan dan siyasa yana da wani abu da yake da bukatar a isar da shi ga jama’a,  idan ya biyo ta wajenmu za mu hadu da shi mu yi don manufarmu dai a taimaka wa jama’a.