✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar Dangote ta tallafa wa wadanda rikicin Ile-Ife ya shafa da Naira miliyan 50

Gidauniyar Dangote ta bayar da tallafin kudi Naira miliyan 50 domin rabawa ga mutane 2 20 da suka yi asarar tsabar kudi da kadarori a…

Gidauniyar Dangote ta bayar da tallafin kudi Naira miliyan 50 domin rabawa ga mutane 2 20 da suka yi asarar tsabar kudi da kadarori a wajen rikicin kabilanci a tsakanin Yarbawa da Hausawa na ranar 8 ga watan Maris da ya gabata a garin Ile-Ife.  Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi shi ne ya jagoranci tawagar Gidauniyar a karkashin Shugabar Gidauniyar Dangote, uwargida Zuwaira Yusuf zuwa mika tallafin da suka yi da hadin gwiwar Ooni na Ife da Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.

da yake jawabi a gaban dimbin jama’a a fadar Ooni na Ife, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya jinjina wa Ooni na Ife a game da hanzarta daukar matakin sanar da Sultan na Sakkwato da shi kansa Sarkin Kano halin da ake ciki a lokacin da ake cikin rikicin, tare da matakin sanar da jami’an tsaro da suka kwantar da al’amarin tare da kama wasu da ake zargin suna da hannu wajen haddasa rikicin kafin ya kazanta. 

“A lokacin da Ooni na Ife ya sanar da mu halin da ake ciki dukkanmu Sultan na Sakkwato da ni kaina mun yi tafiya zuwa kasashen waje. bayan na dawo sai na kawo ziyarar gane wa idanuna komai, a inda muka dunguma tare da Ooni na Ife zuwa wajen da aka yi rikicin. Na ga konannun gidaje da shaguna da bayanan asarar rayuka da kadarori da aka yi mana, abin gwanin ban tausayi. Hakan ne ya sa na sanar da Alhaji Aliko Dangote domin ya tallafa wa wadanda rikicin ya rutsa da su. Aliko Dangote ya amsa rokon da na mika masa shi ne dalilin sake dawowa da na yi zuwa Ile-Ife domin bayar da tallafin nasa.”

Alhaji Muhammadu Sanusi ya ce, a wancan lokaci da aka yi wannan rikicin kabilanci tsakanin Yarbawa da Hausawa,  daukacin sarakunan Arewacin kasa sun ki cewa komai a game da al’amarin ne domin guje  wa kazantar al’amarin. duka jawaban da Sarkin Kano da Ooni na Ife suka yi a wajen wannan taro kafin su mika cakin kudi ga mutanen da suka samu tallafin, sun mayar da hankali ne a game da samar da hadin kan jama’a da zai kawo kwanciyar hankali da zama lafiya a Najeriya, inda suka nuna matukar bakin ciki da aukuwar irin wannan rikici a tsakanin al’ummomin da suka shafe shekaru fiye da 200 suna zaune tare. Sarakunan sun hango cewa zama bisa teburi daya domin warware matsaloli a tsakanin jama’a ita ce hanya mafi sauki wajen samar da dunkulalliyar kasar Najeriya a maimakon kashe-kashen rayuka da kone-konen kadarori na ba gaira ba dalili. Sarakunan sun yi amfani da wannan dama wajen yin addu’ar samun koshin lafiya ga Shugaba Muhammadu buhari.

Shugabar Gidauniyar Dangote Uwargida Zuwaira Yusuf ita ce ta wakilaci Alhaji Aliko Dangote a wajen taron mika cakin kudin ga mutanen da suka samu wannan tallafi da aka gudanar a gaban manyan masu rike da sarautu da dukkan masu fada aji na masarautar Ife. 

Sarkin Hausawan Ile Ife Alhaji Abubakar Mahmuda Madagali yana daga cikin mutanen da suka samu wannan tallafi. Kuma ya nuna bakin cikinsa a game da yadda wasu mutane suka bi ta bayan gida domin yin magudin cire sunayen wasu gidaje da shaguna mallakar Hausawa da aka kona da daga cikin jerin wadanda suka samu tallafin. 

A cewarsa: “Mu dai mun bar komai ga hannun Allah (SWT) da muke rokonSa ya kawo mana dauki kuma ya zaunar da kasarmu  Najeriya lafiya.”