✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar Dangote ta tallafa wa mata dubu 23 a Jihar Sakkwato

Gidauniyar Aliko Dangote ta bayar da tallafin Naira miliyan 239.9 ga mata dubu 23,990, inda kowace mace ta amfana da Naira dubu 10 a fadin…

Gidauniyar Aliko Dangote ta bayar da tallafin Naira miliyan 239.9 ga mata dubu 23,990, inda kowace mace ta amfana da Naira dubu 10 a fadin Jihar Sakkwato.

Shugaban Gidauniyar, Alhaji Aliko Dangote ya ce wannan tallafi yana cikin shirinsa na tallafa wa masu karamin karfi.

Alhaji Dangote ya ce a watan azumin bara ma gidauniyarsa ta tallafa wa masu karamin karfi dubu 106 a jihohin Sakkwato da Katsina da Kebbi da Zamfara da abinci da yawan kudinsu ya kai Naira miliyan 300.

Ya ce ci gaba da tallafin ne ya sanya suka zo Sakkwato domin kaddamar da mataki na biyu na tallafin ga matsakaita da masu karamin karfi.

‘A Sakkwato za mu bayar da tallafi ga mata dubu 23,990 da kuma mata ‘yan gudun hijira a Karamar Hukumar Rabah da yawansu ya kai  990. Matan mabukata ne da Hukumar Zakka ta tantance su, kuma za a ba kowaccensu duba 10 domin su yi jarin duk sana’ar da suke so. Hakan na iya tabbata in suka yi sana’a za su samar da wasu kudin shiga a gidajensu kuma za su rage radadin talauci da ke addabar rayuawarsu,” a cewarsa.

Ya nuna gamsuwarsa da aikin Hukumar Zakka da Wakafi da alkawarin cigaba yin hadaka da hukumar domin taimakawa marasa karfi. Ya ba da sanarwar bada karin Naira miliyan 80 da hukumar domin cigaba da shirinta na baiwa masu karamin karfi bashin da bai da ruwa in da suke da kudi miliyan 21.1 don fara shirin.

A jawabinsa Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya gode wa Dangote da gidauniyarsa da fatan za su cigaba da hadaka a ayyukkan cigaban  jama’a.

Sannan ya bukaci wadanda suka samu tallafin da su sanya shi inda ya dace domin yakar talauci da samun cigaba domin nan gaba wasu  su ci gajiyar shirin kamar su. Ya tabbata wannan tallafin yana cikin hanyoyin da za a iya yakar talauci, sannan ya bayar da tabbacin cewa gwamanti za ta cigaba ba da gudunmuwa a kan irin wannan hobbasa.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ta bakin Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Mera ya yabawa Dangote kan taimakonsa ga mabukata, sannan ya nemi wadanda suka samu tallafin da su yi abin da ya kamata domin taimakon iyalansu.